Talla

Yaran da Aka Kashe Bayan Hanifa

Daga: Muhammad Abdallah

ABUJA, NAJERIYA - Bayan kashe Hanifa mutane sun ci gaba da yaɗa hotunan wasu yara da aka kashe bayan kisan Hanifa, yarinyar da wani malaminta ya sace sannan ya kashe ta hanyar sanya mata guba a cikin kwalbar lemu. An ta yaɗa hotunan wasu yaran da aka kashe kafin a kashe Hanifa. Satar yara a garuwan Kano da Kaduna da Abuja da ma wasu sassa na Arewacin Najeriya ya zama ruwan dare, inda ake yaudarar yaran a sace wasu ayi masu fyaɗe sannan kuma a nemi kuɗin fansa wasu kuwa kuɗin fansa ake nema sannan a kashe su. Ko kwanakin baya saida aka kama wani mutum da yake cin naman mutane a garin Gusau dake Jihar Zamfara wanda wani dake yi masa aiki ya sace wani yaro tare da kashe shi. Ga dai jerin sunane wasu yara da aka sace waɗanda ake yaɗawa a dandalin sada zumunta:

 

Haidar Da Aka Sace A Unguwar Na'ibawa Dake Kano

Haidar yaro ne ɗan shekara huɗu, an sace shi a shekarar 2014 a unguwar Na'ibawa dake birnin Kano. An sace Haidar ne a wata makarantar Islamiyya inda yake zuwa ɗaukar karatun addini. An sace shi a daidai lokacin da yake jiran wata yarinya don su tafi gida, sai wani ya ɗauke shi sannan ya tafi da shi. Waɗanda suka sace yaron sun nemi kuɗin fansa, kuma an basu amma bayan biyan kuɗin fansa si suka faɗi wajen da za a je a ɗauki gawarsa.

Kisan haidar ya jefa iyaye cikin ruɗani da tarababbin makomar yaransu, daga bisani jami’an tsaro sun kama waɗansu mazauna unguwar waɗanda ake tuhuma da laifin sace Haidar. Daga bisani bayan an yi shari’a an tabbatar da sa hannunsu wajen sacewa da kashe Haidar sannan aka yanke masu hukuncin kisa.

 

Aisha Sani Da Aka Sace A Tudun Wada Dake Kano

An sace Aisha Sani wadda ake tsamanin shekarunta za su kai biyar zuwa shidda a unguwar Tudun Wada dake Kano, an sace ta ne lokacin da take dawowa daga Islmiyya tare da yan’uwanta, wata mata ce ta rufe fuskarta sannan ta ɗauki Aisha ta kuma tafi da ita. Sai bayan kwana uku sannan aka tuntuɓi iyayenta aka kuma buƙaci su biya naira miliyan ɗari biyu a matasayin kuɗin fansanta.

Bayan nan ɓarayin sun buƙaci mahaifiyar Aisha ta kai kuɗin fansan. Bayan an kai kuɗin fansar sai kuma aka tsinci gawar Aisha an kashe ta sannan aka daddatsa namanta. Har zuwa yanzu dai ba ada tabbacin abinda ya faru bayan kashe Aisha Sani.

 

Yaro da aka sace a  Karkasara dake Kano

An sace wani yaro ɗan shekara takwas a unguwar karkasara dake Kano, an ɗauke yaron ne bayan an haɗa baki da wanda ke raka shi makaranta, cikin waɗanda ake zargi harwa ƙanin mahaifiyar yaron. Waɗanda suka sace shi sun nemi a basu miliyan biyar.

Bayan sun sace shi sai suka bashi wasu ƙwayoyi waɗanda za su ɗauke masa hankali sannan kuma suka ɗaure shi, wahalar da ya sha ne ya yi sanadiyar mutuwarsa, sannan daga baya suka binne shi a cikin wani kango kuma suka rage yawan kuɗin fansan zuwa naira dubu ɗari.

An samu kama su ne bayan sun zo karɓar kuɗin fansan sannana aka tuhume su, duk ɓarayin da suka sace wannan yaro matasa ne yan ƙasa da shekara ashirin, yanzu haka an gurfanar da su gaban kotu domin fuskantar shari’a.

 

 Wata Uwa Da Ta Kashe Yayanta Guda Biyu A Unguwar Sagagi Dake Kano

Wata mahaifiya ta kashe yaranta guda biyu a garin Kano, mahaifiyar ta kashe yaranta guda biyu namiji mai suna Yusuf mai shekara biyar da mace mai suna Zahra’u mai shekara uku a unguwar Sagagi dake Jihar Kano. Mahaifiyar ta kashe ‘ya’yanta ne sakamakon saɓanin da ta samu da mijinta saboda ya yi mata kishiya. Saidai wata majiya na cewa mahaifiyar da ta kashe ‘ya’yanta tana fama da rashin lafiyar da ta shafi iska ne.

Saidai an tabbatar da cewa mahaifiyar ta kashe yaranta ne ta hanyar sassara su da wuƙa amma dai uwar ta ce yaran ne suka ɗauko wuƙa da niyar su kashe ta ita kuma sai ta kare kanta. Bayan ta kashe su ne kuma aka kai ta asibitin taɓin hankali don duba lafiyarta. Wannan lamari ya zama abun al’ajabi saboda ba a saba ganin irin wannan kisa ba.

 

An Sace Mohammed Kabiru Unguwar A Badarawa Dake Kaduna

An sace Mohammadu Kabir a unguwar Badarawa dake Kaduna, yaro ɗan shekara shidda dai wasu mutane ne suka sace shi sannan suka gudu da shi zuwa Jihar Kano. Daga bisani ɓarayin da suka sace yaron sun kira sannan suka nemi kuɗin fansa.

Sun nemi a basu naira miliyan talatin amma sai suka rage inda aka daidaita za a basu miliyan ɗaya. Bayan sun karɓi kuɗin ne sai suka kashe yaron. Jami’ai sun tsananta bincike inda aka kama mutum huɗu duk maƙwabtan su Mohammad da zargin sacewa da kashe shi.

Daga bisani dai jami’ai sun gurfarnar da waɗanda ake zargi da kashe Mohammad a gaban ƙuliya.

 

An Sace Husnah Garin Zariya

An sace Husnah a garin Zariya, an fara samun labarin satar yarinyar ne a kafafen sada zumunta daidai lokacin da ake tsaka da alhinin rashin Hanifa.

Mahaifin Husnah mai suna Alhaji Wa'alamu mai riƙe da sarautar Uban Dawaki ya tabbatar da cewa an sace ƴarsa ne tun a ƙarshen shekarar da ta gabata, inda ta shafe kwana arba’in da ɗaya a hannun waɗanda suka sace ta.

Ɓarayin da suka sace Husnah sun nemi kuɗin fansa har naira miliyan uku da rabi kuma an basu kuɗin saidai basu sako yarinyar ba.

Da jami’ai suka tsananta bincike sai aka kama wani mutumi wanda maƙwabcinsu ne ana zarginsa da sace Husnah, mutumin ya amsa laifinsa inda ya ce, ya sace Husnah a ƙofar gidansu daidai lokacin da aka aike ta.

Saidai ɓarawon ya sace Husnah ya bayyana cewa ya sace ta ya kuma kashe ta tare da abokan aikinsa, saidai har zuwa rubuta wannan rahoto bai bayyana inda ya rufe gawarta ba bai kuma bayyana abokan da suka yi aikin tare ba.

 

An Kashe wata yarinya bayan an yi mata fyaɗe sannan aka jefara rijiya a Rigasa dake Kaduna

An kashe wata yarinya mai shekara takwas tare da jefata rijiya a Rigasa dake Kaduna, yarinyar ta yi ɓatan dabo ne a unguwarsu, sannan iyayenta da jami’ai suka tsananta bincike inda daga bisani aka ga gawarta a wani gida dake unguwar dake maƙwabtaka da gidan iyayenta. An ga gawar yarinyar ne a cikin wata rijiya, daga bisani aka kai gawar asibiti sannan aka bincika aka tabbatar da cewa an yiwa yarinyar fyaɗe sannan aka kashe ta aka kuma jefa gawarta cikin rijiya.

Daga bisani, an kama wani mutum da ake zargi da sace yarinyar kuma shi mutumin maƙwabcinsu ne. an dai gurfanar da shi gaban ƙuliya.

Wasu Labarai:

  1. Jiragen Yaƙi Na Super Tucano Sun Kashe Kwamandan Iswap
  2. Wani Matashi Ya Rataye Kansa A Jigawa
  3. Wasu Matasa Sun Ƙona Makarantarsu Hanifa Yarinyar da Wani Malaminta Ya Kashe A Kano

Post a Comment

0 Comments