Daga: Muhammad Abdallah
KANO,
NAJERIYA — Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta
tabbatar da cewa wasu matasa sun kona makarantar su Hanifa Abubakar, yarinyar
nan 'yar shekara biyar da ake zargin mai makarantar da yi mata kisan gilla ta
hanyar bata guba da cikin kwalbar lemu ta sha sannan ya saka ta cikin buhu ya
kuma binne ta a ɗaya daga cikin harabar makarantarsu, daga bisani kuma ya yi ta
tsorata mahaifan Hanifa don su bashi kuɗin fansarta.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar SP
Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida faruwar haka a shafinsa na Facebook inda ya
ce, matasan sun kona makarantar ce da tsakar daren Litinin. Saidai ya ƙara da cewa,
har yanzu ba su kama waɗanda ake zargi da aikata ta'asar ba.
Malam
Abdullahi ya bayyana cewa, yana da yara guda biyar, cikinsu ne zai ɗauki Fatima
ya ba iyayen Hanifa, haka kuma ta ɓangaren iyayen Hanifa wasu daga cikin ‘yan uwan
mahaifinta sun kira Malam Abdullahi da niyar su yi magana da mahaifiyar Fatima,
amma daidai lokacin ya fita sallah. Ya zuwa yanzu dai Arewa News ba su ji daga
bakin Malam Abdullahi ba ko mahaifan Hanifa sun sake tuntuɓarsa bisa
wannan kyakyawan ƙuɗuri nasa.
A ranar
Alhamis ne dai aka gano gawar Hanifa bayan wani malamin makarantarsu ya sace ta
a watan Disamba sannan ya kashe tare da binne ta a ɗaya daga
cikin gine-ginen makarantar.
Malamin dai
ya amsa laifinsa a hannun 'yansanda sannan kuma gwamnatin Jihar Kano da ke
Arewacin ƙasar ta rufe
makarantar da malamin yake koyarwa.
Kisan Hanifa
ya zama wani batun da aka fi tattaunawa a sassa daban-daban na cikin ƙasar, inda
iyaye suke alhini tare da jimamin baiwa malamai amanar ya’yansu. Irin
wannan salon satar mutanen don karɓar
kuɗin fansa bai
cika faruwa ba. Haka kuma, malamin ya ɓullo
da wani sabon salo ne wanda zai ƙara
saka tsoro a zukatan iyayen yara musamman a Arewacin ƙasar inda
harkokin tsaro suka taɓarɓare duk da
cewa gwamnati da Jami’an
tsaro na iya ƙoƙarinsu wajen
tabbatar da tsaro.
Wasu Labarai:
0 Comments