Talla

Wani Ministan Abuja Ya Kamu Da Cutar Coronavirus

Daga: Hauwa'u Bello
1 Janairu, 2022

ABUJA, NIJERIYA - Wani Ministan Babba a birnin tarayyar Nijeriya mai suna Mallam Muhammad Musa Bello ya kamu da cutar Corona cutar da ke sarƙe numfashi.

Mai magana da yawun ministan Anthony Ogunleye ya ce, ranar ashirin da takwas ga wannan watan Disamba ne ministan ya fara jin alamun cutar sarƙewar numfashu, inda ya yi ta fama da mura mai tsanani.

Mai magana da yawun Ministan ya faɗi haka ne a wata takarda da ya sanya wa hannu.

Bayan Ministan ya ji alamun sai ya kai kansa ga jami'an kiwon lafiya don gwaji, bayan an gyada shi, sakamakon ya nuna cewa Ministan yana ɗauke da cutar Corona cutar da aka fi sani da Covid-19 ko kuma cutar sarƙewar numfashi. 

Yanzu dai Ministan ya keɓe kansa inda likitoci ke kula da lafiyarsa.

 Sanarwar ta ƙara da cewa, yanzu Ministan yana cikin koshin lafiya kuma yana samun sauƙi sosai.

Ministan Abujan dai ya karbi allurar rigakafin Coronavirus har sau biyu, ya kuma nemi mazauna birnin da suma suje a masu rigakafin.

Cutar Coronavirus cuta ce da ta girgiza duniya wadda ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutane. Cutar ta taso daga Ƙasar China inda dubunan mutane suka mutu sanadiyar cutar a faɗin duniya.

Post a Comment

0 Comments