Talla

Wani Matashi Ya Rataye Kansa

 Daga: Muhammad Abdallah

JIGAWA, NAJERIYA - Wani mutum ya rataye kansa a Jihar Jigawa. Jihar dai tana ɗaya daga cikin jahohin Arewacin Najeriya da aka fi samu mace-mace ta hanyar ɗaukai rai.

Mutum ɗan shekara 25 ya kashe kansa ta hanyar rataya a ƙaramar hukumar Taura.

Kakakin ƴansanda a jihar ASP Lawan S Adam ne ya tabbatar da aukuwar al'amarin. ASP ya ce, mutumin wanda da farko aka bayar da rahoton batansa, an same shi ya rataye a wata bishiya da ke bayan gari a ƙauyen Zangon Maje dake ƙaramar hukumar, mutumin ya yi amfani da wandonsa a matsayin igiya sannan ya rataye kansa a saman bishiyar. Matashin ya kashe kansa ne a jiya Litinin wato 24 ga watan Janairu, 2022.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar ya ƙara da cewa,

"A ranar Litinin ne Hakimin Kwalam, Alhaji Muttaka Uba ya kira ya kuma inda faɗawa hukumar ƴansanda cewa wani mutum mai sjna Naziru Badamasi ɗan shekara 25 dake ƙauyen Tsadawa a ƙaramar hukumar Taura, wanda kuma yake da tabin hankali, ya bata bayan ya bar gida a ranar da misalin karfe goma sha biyu da rabi na ranar".

Ya ƙara da cewa,

"Daga bisani ne aka gano mutumin ya rataye kansa a bayan garin Zangon Maje, wanda shi ma a yankin wannan karamar hukuma yake".

Kakakin ya ce, da samun wannan labari aka tura jami’an ƴansanda suka je wurin, inda suka ɗauko gawar suka kai ta babban asibitin Ringim, nan nd likita ya tabbatar da cewa mutumin ya rasu.

Jami’in ya kuma ce, daga baya ne suka miƙawa ƴan uwan mamacin gawar domin yi masa jana’iza, a bincike da ƴansanda suka gudanar babu wanda ake zargi da aikata kisan.

Wasu Labarai:

  1. Wasu Matasa Sun Ƙona Makarantarsu Hanifa Yarinyar da Wani Malaminta Ya Kashe A Kano
  2. Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Ɓarayin Daji A Yankunan Zamfara
  3. Wani Bawan Allah Ya Ƙuduri Aniyar Ba Mahaifan Hanifa Kyautar Ɗiyarsa

Post a Comment

0 Comments