Talla

Wani Mahaifi Ya Yi Wa Agolarsa Mai Shekara 3 Fyaɗe

Daga: Muhammad Abdallah 

BAUCHI, NAJERIYA - Rundunar ƴansandan Najeriya, ta ce ta kama wani uba da ake zargi da yi wa ƴarsa mai shekara 3 fyaɗe a unguwar Doya dake ƙaramar hukumar Kirfi a cikin Jihar Bauchi. Mahaifiyar yarinyar ce ta kai ƙara a ofishin ƴansandan yanki, inda ta shaida cewa,

''Mijina Ali Lawan ya buƙaci in kai masa tabarma don ya kwantar da ita ta yi barci”.

Ta ci gaba da cewa,

''Ina komawa ɗakin na tarar yarinyarmu rai hannun Allah, tana da haraswa ga tsakanin gumi a jikinta”

Ta ce,

“Bayan nan kuma, gabanta ya yi kumburi sosai yana ta zubar da jini”

Daga bisani ƴansanda sun kai yarinyar babbar asibitin garin don samun kulawa. Bayan likitoci sun yi bincike sun tabbatar da cewa fyaɗe aka yi wa wannan yarinya. Daga nan sai rundunar ƴansanda ta bazama don kama mahaifin yarinyar, an kuma samu nasarar kama shi, yanzu haka yana tsare inda ake yin bincike kafin a kurfanar da shi gaban kotu.

Ko a kwanakin baya ma sai da aka kama wani mutumi mai shekara 45 da zargin yi wa wata yarinya ƴar shekara 7 fyaɗe a garin Faggo da ke ƙaramar hukumar Shira a jihar ta Bauchi.

Ɗan majalisar dake wakiltar yankin Honarabul Bello Muazu Shira, wanda ya tayar da batun a majalisar dokokin jihar ya yi kiran a gaggauta kama mutumin kan zargin yi wa ƴar shekara bakwai fyaɗe.

Ɗan Majalisar ya ce,

"Ya yi wa yarinyar barazana da makami ya yi mata fyaɗe,"

A baya-bayan nan gwamnatin jihar ta Bauchi ta kafa wata doka da ta kira VAPP wadda a turance ake kira Violence Against Persons Prohibition, ta kuma tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da laifin yi wa yara kanana Fyaɗe. Haka ma dokar ta tanadi ɗaurin rai da rai ga wanda ya yi wa babbar mace fyaɗe, da kuma ɗaurin shekaru 20 ga waɗanda suka yi wa mace ɗaya taron dangi.

Al’amarin fyaƙe ya zama ruwan dare a faƙin duniya, inda mutane ke biye wa dokin zuciya suna haiƙe wa ƙananan yara wasu don sha’awa wasu kuwa don cika wani burinsu ko neman duniya ko kuma cika wani sharaɗi da malaman tsubbu suka basu.

Wasu Labarai:

  1. Jarumar Fina-Finai Ta Zargi Kanta Da Ƙin Sake Yin Wani Aure
  2. Abin da nake Dubawa Kafin in Yarda a Sumbace ni a Fina-finai — Queeneth Agbor
  3. 'Yan Bindiga Suna Yin Shigar Mata Don Kai Hari A Yankunan Sokoto

Post a Comment

0 Comments