Daga: Hauwa’u Bello
BAUCHI, NAJERIYA — Wani Mahaifi ya yi niyar ba
mahaifan Hanifa ɗiyarsa mai suna Fatima don rage masu raɗaɗi daga cin amanar da
aka yi masu. Hanifa dai yarinya ce ƴar shekara 5 wadda wani malaminta ya sace
sannan ya yi mata kisan gilla ya kuma binne ta a ɗaya daga cikin kangayen
makarantarsu.
Malam Abdullahi Ahmed Latus mazauni ne a ƙaramsr
hukumar Darazo dake Jihar Bauchi ya faɗi cewa tuni ya fara ƙudurta bayar da ɗiyarsa
da mahaifan Hanifa domin rage masu kewar rashin ɗiyarsu.
A wata tattaunawa da wakilin Arewa News ya yi da
Malam Abdullahi ta wayar salula, mahaifin Fatima ya ce,
“Bisa tausawa da kuma jajantawa wannan bayin Allah, ɗiyarsu
ɗaya aka yi masu wannan ci amana, to wannan ne yasa tunda Allah mu ya bamu su,
naga bari na sadaukar da Fatima ga iyayen Hanifa, idan sun amince su ɗauketa
don ɗebe kewar ɗiyarsu”
Ya ƙara da cewa,
“Wannan kuma ya yi shi ne tsakaninsa da Allah (SWA)”
Mahaifin Fatima ya bayyana cewa, tun lokacin da ya
samu labarin kisan Hanifa bai sake samun natsuwa ba, babban abinda ya fi tayar
masa da hankali shi ne, yadda Malamin ya je inda ya ɓoye Hanifa cikin dare ya
tashe ta da zummar zai kai ta wajen mahaifinta, amma sai ya zuba guba a cikin
robar lemu ya bata, ta sha.
Malam Abdullahi ya bayyana cewa, yana da yara guda
biyar, cikinsu ne zai ɗauki Fatima ya ba iyayen Hanifa,
haka kuma ta ɓangaren iyayen Hanifa wasu daga cikin ‘yan uwan mahaifinta
sun kira Malam Abdullahi da niyar su yi Magana da mahaifiyar Fatima, amma
daidai lokacin ya fita sallah. Ya zuwa yanzu dai Arewa News ba su ji daga bakin
Malam Abdullahi ba ko mahaifan Hanifa sun sake tuntuɓarsa bisa wannan kyakyawan
ƙuɗuri nasa.
A ranar Alhamis ne dai aka gano gawar Hanifa bayan
wani malamin makarantarsu ya sace ta a watan Disamba sannan ya kashe tare da
binne ta a ɗaya daga cikin gine-ginen makarantar.
Malamin dai ya amsa laifinsa a hannun 'yansanda
sannan kuma gwamnatin Jihar Kano da ke Arewacin ƙasar ta rufe makarantar da
malamin yake koyarwa.
Kisan Hanifa ya zama wani batun da aka fi tattaunawa
a sassa daban-daban na cikin ƙasar, inda iyaye suke alhini tare da jimamin
baiwa malamai amanar ya’yansu. Irin wannan salon satar mutanen don karɓar kuɗin
fansa bai cika faruwa ba. Haka kuma, malamin ya ɓullo da wani sabon salo ne
wanda zai ƙara saka tsoro a zukatan iyayen yara musamman a Arewacin ƙasar inda
harkokin tsaro suka taɓarɓare duk da cewa gwamnati da Jami’an tsaro na iya
ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaro.
Wasu Labarai:
0 Comments