Daga: Muhammad Abdallah
ABUJA,
NAJERIYA - Wani ɗalibi da hukumar makaranta ke neman ɓoye sunansa ya yanka Jibril
Sadi Mato da reza a maƙogoro lamarin da yasa aka kai Jibril asibiti tare da yi
masa tiyata a wuya. Dukkan ɗaliban guda biyu sun fito daga makarantar Elkanemi
College of Theology take Jihar Borno.
Ɗalibin dai
yana gaba da su Jibril, inda ake tsammani ɗan aji biyar ne, ya aiki Jibril
wanda ake wa laƙani da Ramadan, amma sai Ramadan bai yi aikin da ɗalibin ya
sanya shi ba, wanda yasa ɗalibin ya yi fushi sannan ya yanki Ramadan da reza a
maƙogoro.
Yan’uwan
Ramadan ne suka kai ƙorafin faruwar al’amarin a caji ofis. Ƴan uwan suna zargin
wani Ɗalibi da ke ajin gaba da na Jibril ne ya raunata shi a wuya ta hanyar
yankansa da reza har sai dai ya yi illa ga maƙogwaronsa.
Yar’uwar
Ramadan ta ce,
"Ramadan
an yanke shi ne a wuya, wanda hakan ya haifar masa da raununka masu tsanani, a
halin da ake ciki yana kwance a asibiti rai hannun Allah. Kuma ko ya tashi daga
jinyar ba lallai ya sake ci gaba da iya magana ba”.
Ta ƙara da
cewa,
"Wanda ya
yanka shi shima yaro ne ɗan makarantarsu saidai kuma ana so a ɓoye abin, don
ita kanta hukumar makaranta ba ta sanar da faruwar lamarin ba”.
Ta kuma ce,
"Muna so
gwamnati ta yi bincike ta gano ainhin abin da ya faru sannan a gurfanar da mai laifin
a kuma yi masa hukunci,"
Yaron da dangin
Ramadan ke zargi da yanka shi, wani ɗan gata ne da ya fito daga gidan masu
hannu da shuni, ƙila wannan ne ya sa shugabannin makarantar suke ta rufe
maganar. Wata majiyar ta ce, shugabannin makarantar sun fara sauya maganar,
suna cewa wai rauni kawai Ramadan ya ji, ba wani ne ya yanka shi ba.
Ba wannan ne
karon farko da ake samun irin wannan cin-zali ko fin ƙarfi da manyan ɗalibai
suke nuna wa ƙanana a makarantar ba, kuma sau da yawa ba a ɗaukar mataki na
kaiwa ga hukuma.
1 Comments
Allah ya kyauta
ReplyDelete