Talla

Ƙungiyar masu kai Abinci ta bi umarnin IPOB ba za su Ƙara kai Abinci Kudancin Ƙasar Nijeriya ba

Daga: Hauwa'u Bello

5 Janairu, 2022

ABUJA, NIJERIYA - Ƙungiyar masu fataucin dabbobi da kayan abinci a Nijeriya ta ce ta shirya don barin kai shanu da kayan abinci zuwa kudancin ƙasar. 

Ƙungiyar ta faɗi haka ne bayan masu neman kafa ƙasar Biafra ta fitar da wasu dokoko cikinsu hadda barin cin naman shanu da hana rera waƙokin sallawa ƙasa.

Shugaban ƙungiyar wato Kwamared Muhammad Tahir, ya ce,

Mataki da IPOB ta ɗauka ba su komai a jikinsu ba.

Ya ƙara da cewa,M

una son Nijeriya ta zama ƙasa ɗaya, amma idan ya zama suna ganin hakan ta fi zame masu dai-dai, ta fi nono fari.

Ya kuma ce,

Wannan abun da ake kaiwa fa dukiya ce a ke kai masu ba tsiya ba, abinci ne a ke kai masu ba guba ba.

Saboda haka wanda ka ke kai wa abinci ya ce ba ya ƙaunar abincin sai ka ce dole ne lallai ko da yana kashe ka sai ka kai masa?

Shugaban ya ce, ba za su iya jurewa rashin abinci ko na kwana ɗaya ba, don haka dole su janye wannan farafagandar da suke yaɗawa.

Daga cikin dokoki bakwai da Ƙungiyar IPOB ta fitar akwai; kamfe don neman sakin fursunoninta da ake tsare da su da fara zanga-zanga a manyan birane da ke faɗin duniya da hana rera taken ƙasa a makarantu da hana cin naman shanu.

Wasu daga cikin dokokin za su fara aiki ne daga watan Afrilu.

Post a Comment

0 Comments