Talla

Tarihin Sarautar Sardauna

 Daga: Bello Hamisu Ida

SOKOTO, NAJERIYA - Sardaunan Sakkwato marigayi Ahmadu Bello a cikin tarihin rayuwarsa, ya bayyana cewa ita sarautar Sardauna daga Sakkwato ta samo asali. Babu wata masarauta da ta taɓa amfani da wannan sarauta kafin Sakkwato.

Amma kuma dangane da ma’anar kalmar yana da wahalar fassara kai tsaye. Sai dai a kan danganta ma’anonin kalmomin muƙaman sarautun Hausa da irin ayyukan da suke yi. Misali Waziri, shi ne shugaban gwamnati ko firaminsita. Madaki, mai kula da dawakai, Magajin Gari mai lura da ƙasa, ko Makama wanda ke ladabtarwa.

Ana iya cewa asalin sarautar Sardauna daga Sakkwato ne. Marigayi Ahmadu Bello ya bayar da ƙarin haske a kan sarautar yana cewa ana keɓanta ta ga ‘ya’yan sarki ne kaɗai, kuma aikin da mai sarautar ke yi shi ne duk lokacin da aka fito fagen daga Sardauna shi ne ke shugabantar ‘ya’yan sarki ya yi share wa kwamanda fage. Haka kuma shi ne zai ɗauki alhakin bada cikakkiyar kariya ga sarki idan yaƙi ya rincaɓe rana ta ɓaci.

Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Ɗan Shehu Mujaddadi, wanda ya yi halifancin Daular Islam ta Sakkwato daga shekarar 1817 zuwa 1837 shi ne ya fara ba da sarautar Sardauna. Ya naɗa Halilu Ɗan Hassan Ɗan Shehu Usman Mujaddadi a matsayin Sardauna na farko a duk faɗin Bilad a Sudan, wanda ya haɗa da Najeriya da wani yanki na ƙasar Nijar da Chadi da Mali da Ghana.

Wanda suka riƙe sarautar Sardaunan Sakkwato bayan ta farko sun haɗa da; Abdurrahman Jalau da Abdul ɗan Mamman daga kansu sai aka baiwa mai alfarma sakrin Musulmi Abubakar na uku. Ya riƙe Sardaunan Sakkwato kafin ya zama sarkin Musulmi a shekarar 1934 Sardaunan shi ne Alhaji Abubakar Alhaji.

Akwai saɓanin bayani da wasu ke cewa su ma Sakkwatawa aro wannan sarauta ta Sardauna daga masarautar Gobir. Shahararren mawaƙin nan Ibrahim Narambaɗa a waƙensa na Sardaunan Gobir, yana cewa,

“Na riƙa ka girma Abdu ƙanin Mai Daga, kanda mu san kowa kai mun sani Sardauna.”

Sir Ahmadu Muhammadu Bello wato Ahmadu Bello an haife shi ne a 12 ga watan shekarar alif 1910 a karaman hukumar Raba dake garin sakwato yana da lambar yabo ta KBE muƙamin Sardauna kuma shi ne tsohon Firimiyan Arewacin Najeriya.

kuma yarike sarautar Sardaunan a jahar Sokoto. An haifi Sir Ahmadu Bello sardauna a garin Raba dake cikin lardin Sokoto a shekara ta alif dubu daya da dari tara da goma (1910). Duk da cewa Sardaunan sokoto Sarauta ce tashi a jihar sokoto, Amma sunan ya zama kamar wani inkiya a gareshi inda ya shahara wajen amsa shi a ciki da wajen nijeriya.

 Karin wasu Tarihin:

  1. Yadda Aka Kashe Sardaunan Sokoto Muhammadu Bello
  2. Tarihin Aliku Dangote wanda ya fi kudi a Afirika
  3. Mutum da Muhallinsa

Post a Comment

0 Comments