Talla

Sojojin Najeriya sun kuɓutar da matafiya a Kaduna

13 Janairu, 2022

Daga: Muhammad Abdallah

KADUNA, NAJERIYA - Sojojin Najeriya sun kuɓutar da wasu mutane da aka sace a hanyarsu. Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kuɓutar da mutume ashirin d shidda waɗanda aka yi garkuwa, Sojojin sun samu nasarar ne a wani samame da suka kai a bisa hanyar  Birninn Gwari zuwa Kaduna, Sojojin dai sun kai samamen ne a maɓoyar da aka aje matafiyan a ranar laraba.

Kakakin rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ya yi ƙarin bayani inda ya ce, 

"Mun samu wannan nasarar ne bayan dakarunmy sun hangi wasu motoci biyar babu fasinja a ciki a kusa da Anguwar Yako, abin da ke nuna akwai yiwuwar an yi garkuwa da fasinjojin dake cikin motocin".

Wani direba ya yi ƙarin bayani inda ya ce, an harbe wani fasinjansa lokacin da 'yan fashin suka tare hanya tsakanin Birnin Gwari da Kaduna da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Laraba.

Direban ya ƙara da cewa,

"Sojojin sun zo sun tambaye mu inda ɓarayin suke kuma mun nuna musu. Suna cikin yin harbe-harbe kuma sai ga mutane suna fitowa daga daji,".

Matafiyan sun bayyana cewa an faɗa masu an ga gawar wata mace a cikin daji, sannan wata mata ta yi ƙorafin cewa an kashe mijinta tana roƙon a taimaka mata a ɗauko gawarsa a dajin.

Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Wasu Labarai:

  1. Wani Bawan allah ya Roƙi QS Yakubu Manni Ya fito Takara
  2. Gwamnati ta Janye Haramcin Amfani da Twitter
  3. Yan Adaidaita Sun Janye Yajin Aiki a Kano

Post a Comment

0 Comments