Talla

Shugaban Ƙasa Ya Ayyana ‘Yan bindiga A Matsayin Ƴan Ta’adda

 Daga: Hauwa'u Bello

05 Janairu, 2022

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ayyana Ƙungiyoyin Ƴan Bindiga da ke kai hare-jare a Arewacin Ƙasar a matsayin Ƴan Ta’adda.

Sanarwar ayyanawar na ƙunshe ne a cikin takardar Gwamnatin Tarayya da ke bada bayanin cewa yanzu ƙungiyar ta zama ta ƴan ta'adda kuma ta hana duk wani ɗan ƙasa alaƙa da ƙungiyar, duk wanda ya taimaka masu ko ya shiga cikinsu shima ya zama ɗan ta'adda.

Hakan na zuwa ne bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana ƴan bindigar a matsayin ƴan ta’adda biyo bayan wani ƙudiri da Gwamnatin Tarayya ta shigar a gabanta ta hannun ma’aikatar shari’a.

A ranar 26 ga Nuwamba, 2021, Mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya amince da bukatar ayyana ayyukan ƴan bindigar a matsayin ayyukan ta’addanci.

Tun a ranar Talata ne dai, Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ya ce, ofishinsa na ƙoƙarin ganin bayan wani hukunci da kotu ta yanke wanda ya umarci gwamnati ta ayyana ƴan bindigar a matsayin ƴan ta’adda.

Barayin daji dai suna satar mutane don karɓar kuɗin fansa tare da kashe duk wanda ya gagara biyansu. Ko a watannin da suka gabata saida wani ɗan fashin daji ya ƙone wasu mutane da suka yi hijira don sun kasa biyan harajin da ya sanya masu.

Kodaye a satin nan ne ɗan fashin dajin ya sako duk mutanen da ya yi garkuwa da su a yunƙurinsa na yin sasanci da gwamnati.

Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Post a Comment

0 Comments