Shaharar Yaro Cinye-gari A Bikin Budar daji
Daga: Littafin Hikimarka Jarinka na Bello Hamisu Ida
Zamanin wani sarki na haɓe, kafin zuwan Musulumci ƙasar Hausa, a kusa
da binnin Katsina akwai wani ɗan ƙaramin ƙauye da Allah ya yi wa albarkar
Jama’a mai suna Battagari. Mafi yawan mutanen garin Mafarauta ne da Bokaye da
suke zuwa cin zango su wuce.
A wannan garin ne ake taruwa duk ƙarshen shekara bayan saukar ruwa ayi bikin Buɗar daji, watau a nemi albarkar wannan shekara da neman tsari daga cututuka a wajen ubangijin da mutanen suke bauta ma wa.
A cikin garin Battagari, akwai wani ƙaƙƙarfan mutum maji ƙarfi. An ce da kansa yake kashe giwa ya kawo namanta gida, sunansa Baka. Shaharar wannan mutumin ne ta sa mutanen garin suke biyayya a gare sa, har yake masu jagoranci a wajen bikin buɗar daji.
Mutanen garin Battagari suka rinƙa kiransa Sarkin Dawa. An ce babu wanda ya kai shi iya jan kwari da baka. Ya sha harbo idon zakanyar da take shayarwa daga nesa.
Allah
ya albarkanci Sarkin Dawa da ‘ya’ya masu tarin yawa ‘ya’yansa tamanin da shidda,
ga mata bila adadin matansa talatin da tara, ta ɓangaren dukiya kuwa ba a cewa
komai. Matarsa ta goma sha uku ɗiyar
wani boka ce, wacce bokan ya aurar da ita ga Sarkin Dawa don ta gaje sarautar
gidansa. Bayan shekara da auran Talle Ɗiyar boka, ta samu juna biyu ta haifi ɗa
namiji, aka sanya masa suna Cinye-gari, watau ma’ana ya kwace garin Battagari
daga hannun ubansa Sarkin Baka. Ranar suna Sarkin Dawa ya cire wata laya daga ƙugunsa
ya ɗaura wa ɗansa layar a ƙugu.
Bayan yaro ya tasa
ya kai shekara uku, rannan sai mahaifiyarsa ta kwanta barci. Talle ta yi mafarkin
wasu mutane sun zo suna mata ishara da cewa,
“Ɗanki Cinye-gari ba zai mutu ba har sai lokacin da aka ƙone layar
da ubansa ya ɗaura masa a ƙugu, in kuwa duniya ta ɗaukaka sai ya zama Sarkin
duk Ƙasar Hausa.”
Talle ta ɗimauta da
wannan mafarki, tana farkawa ta kwance layar dake ƙugun Cinye-gari ta ɓoye,
watau ɗai ɗanta ba zai taɓa mutuwa ba tun da ta ɓoye laya.
Cinye-gari ya taso
cikin sa’o’insa ƙaƙƙarfa, ba mai iya karawa da shi. Wasu lokutan har buge
manyansa yake yi. Haka ya tashi cikin izgili da raina mutane, shi ga mai ƙarfi.
Ita kuwa uwarsa sai ta zagi mutum idan ya taso ta haɗa shi da Cinye-gari, ta san
shi ne mai duniya ba zai taɓa mutuwa ba. Cinye-gari yana da shekara bakwai aka
tashi yin bikin Buɗar Daji.
Ranar buɗar daji ta
zo, manyan mafarauta, bokaye da maharba suka taru bakin daji, makaɗa da mawaƙa da
‘yan goge suka yi ta kirari tare da zuga maza.
Da Rana ta yi sanyi Sarkin baka ya yi umurni aka shiga dajin farauta, nan kowa ya shiga nuna tasa bajintar. Karon farko Cinye-gari ya samu sa’ar kashe zaki, ba’a jima ba ya sake kashe kura, bai fito dajin ba sai da ya kashe barewa uku, karen daji da Zomaye, ya jawo su ya kawo bakin ɗaji.
Duk wanda ya kawo namansa babu wanda ya kaso abin da Cinye-gari ya kashe, aka shiga kuranta sa ana masa kirari, take mahaifinsa ya ba shi sarautar wazirinsa.
Baƙin ciki wajen danginsa ba a cewa komai, kishiyoyin uwarsa kuwa suka huro wuta, suka shiga bin bokaye, suna son kashe Cinye-gari don kar ya karɓe gida.
Wata rana matar Sarkin Baka mai bi
wa Talle ta laɓe bayan ɗakin Talle, ta ji tana ce wa Cinye-gari,
“Duk su yi iyakar tugunsu, ba za su taɓa gane makasarka ba, babu
wanda ya san makasarka sai ni uwarka. Watau wannan Laya da ka ke gani ina ɓoyewa
ita ce makasarka da zaran ta ci wuta, taka ta ƙare.”
Cinye-gari ya tsorata sosai da jin wannan labari, take ya murɗe kan
uwarsa ya ɗauke laya, ya kai bayan gari cikin wani kogon dutse ya bizne.
Duk abin nan da ke faruwa
wannan mata tana biye da shi, bai sani ba. Yana barin wajen ta shammaci ido ta
shiga kogon ta tone laya ta ɗauke ta.
Wasu Labarai
- Labarin Jatau Mawaƙi
- Labarin Akuya mai Magana
- Labarin Ƙaiƙayi Koma Kan Masheƙiya
- Labarin Na Shiga Ban Ɗauka Ba
- Labarin Sarkin Dawa
- Labarin Aikata Alheri Duk Inda Ka ke
- Labarin Ka So Naka, Duniya Taƙi Sa
- Labarin Ɓarawon Birni Da na Ƙauye
Shi kuwa Cinye-gari ya nufi turakar Ubansa don ya murɗe masa wuya ya
ƙarbi Sarauta da ƙarfi, kafin ya isa wannan mata ta sanya wa layar wuta, yana
daidai ƙofar turakar ubansa layar ta ƙarasa cinyewa da wuta, ubansa ya ji faɗuwar
Cinye-gari, yana fitowa ya ci karo da gawarsa.
Ya yi godiya, daga nan Sarkin Baka ya yi ammana da tsarkin Allah, ya
tabba ta ikon Mai duka ne kawai ya tseratar da shi daga sharrin boka uban
Talle.
Daga nan ya kafa mulkin gaskiya a tsakanin iyalansa da al’umarsa
baki ɗaya. Ya bar fifita wani kan ɗan’uwansa.
0 Comments