Talla

Sanata Aleiro Ya Buɗe Sabon Ofishin APC A Kebbi

#Arewanews

Daga: Muhammad Abdallah

11 Janairu, 2022

KEBBI, NIJERIYA - shugabanci a jam'iyyar APC ba wani sabon abu bane, dukan duk jahohin dake cikin ƙasar suna fama da ire-iren waɗannan rikicin. Ko a Jihar Kebbi rikicin jam’iyyar ya yi tsanani, bayan da tsohon gwamnan jihar Sanata Muhammadu Adamu Aleiro ya buɗe sabuwar hedikwatar jam'iyyar ta jihar. Bayan wani taro da aka gudanar a ranar lahadi an buɗe sabuwar hedikwatar Jam’iyya a cikin Jihar.

Duk da ƙoƙarin da ɓangarensa da na gwamna wato Sanata Atiku Bagudu da kuma kwamitin Abdullahi Adamu ke yin a sasanta ɓangarorin guda biyu, amma hakar ta ƙi cimma ruwa. Amma kuma ɓangaren Gwamna Bagudu ya ce buɗe sabon ofishin a zaman haramtacce ne kuma an buɗe sabon ofishin ba bisa doka ba.

Wasu na ganin wannan matakin na Sanata Aleiro a matsayin wanda zai iya janyo wa jihar ta Kebbi tashin hankalin siyasa, an dai shaidi Jihar da kwanciyar hankali da kuma rashin kawo taƙaddama tsakanin jam’iyyun hammaya tun farko kafuwar siyasar Jihar.

Tsohon gwamnan da Alhaji Bello Bagudu yayan Gwamna Atiku Bagudu da sauran magoya bayansu, sun yi taro sannan taga bisani suka buɗe ofishin. An bude ofishin ne a gidan jigon APC Alhaji Bello Bagudu wan Gwamna Atiku Bagudu.

Alhaji Sani Dododo shi ne kakakin ɓangare Sanata Aleiro, ya ce,

Babban dalilin samun wannan rabuwar kan yana da nasaba da wani taron APC da aka yi a baya inda aka cimma matsaya daban-daban.

Sai dai kakakin jam'iyyar bangaren Gwamna Atiku Bagudu, Alhaji Isa Assalafi ya ce,

Jam'iyyar APC ba ta rabu ba kamar yadda ake faɗa.

Ya ƙara da cewa,

Jam'iyyar APC a Kebbi na nan a haɗe, tsintsiya ce maɗaurinta ɗaya.'

Ga alama dai har yanzu da sauran kallo don kowane ɓangare ya miƙa wa hukumar zaben jihar sunayen ƴan takaransu a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar da kansiloli da za a yi ran biyar ga watan Fabrairu.

 Wasu Rahotanni

  1. Najeriya ta ci Masar 1 - 0
  2. An Kashe Ɓarayi Biyar A Ƙaramar Hikumar Giwa Ta Kaduna
  3. An Dasa Zuciyar Alade ga Wani Mutum Ɗan Shekara 57

Post a Comment

0 Comments