#Arewanews
Daga: Muhammad Abdallah
09 Janairu, 2022
ABUJA, NIJERIYA - Bangaren Dr. Ahmed Gumi ya yi zargin cewa, Jiragen Yaqin Nijeriya na
jefa bama-bamai a kan mutanen da basu ji, basu gani ba a yankin Arewa maso
Yammacin qasar, inda ke fama da tashe-tashen hankulla da varayi masu satar
mutane don karvar kuxin fansa, rundunar sojojin samar ta qasar ta maida amrtani
kan zargin.
Mai magana da yawun Dr. Ahmad Gumi, wato Mallam Tukur Mamu ya yi zargin
cewa, jiragen yaqin saman qasar na jefa boma-bomai kan wasu mutane a yaqin da
rundunar take yi da varayin daji.
Mallam Tukur Mamu yana cikin tawagar Dr. Gummi da suka zagaye dazukan Arewacin
Nijeriyar, don yaxa wa’azi da kuma yin da’awa ga varayin daji da kuma sauran
qauyawa da suke zaune cikin daji. Qauyawan sun yi koken cewa, ba kan varayin
aje jefa bam ba, sau da yawa ana jefawa bisa mutanen da basu ji ba, basu gani
ba.
Mallam Mamu ya nemi gwamnati ta xauki hanyar sulhu da varayin dajin ta
hanyar gano ainihin musabbin wannan tarzoma don magance shi baki xaya.
Amma Hedkwatar rundunar mayaqan saman Nijeriyar ta ce, wannan zargi ne
da bai da tushe balle makama da kuma ke nuna wasu mutane basa farin ciki da
nasarar da ake samu a yaqi da yan bindigar.
Kakakin Rundunar mayakan saman Najeriya Air Commododore Edward Gabkwet,
ya shaidawa muryar Amurka cewa kafin jiragen yaqi su kai hari sai an tabbatar
da ainihin inda yan varayin suke ta hanyoyin tattara bayanan sirri a kimiyance
ta yadda ba yadda za a samu wanda basu aka nufa da harin ba.
Wasu Rahotanni
- Osinbajo Ya Tafi Ghana Don Wakiltar Shugaba Buhari A Taron Ecowas
- Buhari Ya Nemi Mutanen Zamfara Su Ƙara Haƙuri
- Wa Ya Ci Amanar Wani: Gwamna Masari Ko Sanata Babba Kaita?
Garuruwan
Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren varayin
daji masu satar mutane don karvar kuxin fansa. Amma Jami’an tsaro da gwamnati
na iyakacin qoqarinsu don kawo qarshen wannan tashin hankali a Arewacin
Nijeriya.
0 Comments