#Arewanews
Daga: Muhammad Abdallah
09 Janairu, 2022
ZAMFARA, NIJERIYA - Mataimakin
Shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Oisnbajo ya tafi Accra babban birnin ƙasar Ghana
domin wakiltar Shugaba Muhammadu Buhari a wani taro na musamman da Ƙungiyar
Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta shirya.
Mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar wato Laolu Akande ne ya fitar da sanarwar inda ya ce,
Shugabannin ƙasashen yammacin Afrika za su tattauna a wajen taron kan batun siyasar ƙasar Mali.
Bashi
kaɗai ya tafi ba, mataimakin shugaban ƙasan Farfesa Osinbajon ya tafi tare da
ƙaramin Ministan Harkokin Waje na Nijeriya wato Ambasada Zubairu Dada, za su
dawo a yau Lahadi.
Ko
a watan Nuwamba na shekarar 2021 sai da Mista Osinbajo ya je Accra don tattaunawa
kan batu na siyasar Mali da kuma ƙasar Guinea.
Wasu Rahotanni
- Buhari Ya Nemi Mutanen Zamfara Su Ƙara Haƙuri
- Wa Ya Ci Amanar Wani: Gwamna Masari Ko Sanata Babba Kaita?
- Ɓarayi sun sace tsohon jami'in kwastam a Nijeriya
Goodluck
Jonathan shi ne mai shiga tsakani na ƙungiyar ta ECOWAS shima ya tafi Mali a
ranar 5 ga watan Janairun 2022 don tattaunawa da hukumomin ƙasar Mali kan batun
jadawalin miƙa mulki ga farar hula.
0 Comments