#Arewanews
Daga: Muhammad Abdallah
11 Janairu, 2022
ABUJA, NIJERIYA - Kungiyar kwallon kafar Najeriya wato Super
Eagles, ta zura kwallonta ta farko a ragar Masar a wasan da suke yi a gasar cin
kofin nahiyar Afirka. A cikin mintina 30 da take wasan ne ɗan wasa Kelechi
Iheanacho ya zura kwallon. Kwallon da Iheanacho ya zura ya tabbatar da
nasarar da kungiyar Super eagle ta samu ya yi wasan da aka gwabza.
Yan wasa Moses Simon zuwa da Joe Aribo da Maduka Okoye da Mohammed Salah sun taka
muhimmiyar rawa, amma kowane ɗan wasan Super Eagles ya taka leda da niyya ya samu
nasara wanda yanzu suka aika gargaɗi ga sauran kungiyoyi a gasar.
Wannan shi ne karo na tara da za a kece raini tsakanin Najeria da
Masar a gasar cin kofin nahiyar Afirka. Nageriya ta yi nasara a kan
Masar sau uku da canjaras uku, sai dai wasan ƙarshe da suka haɗu a shekarar 2010,
Masar ce ta doke ƙungiyar Super Eagles da ci 3-1.
Wannan shi ne karo na 19 da Super Eagles za ta buga Afcon, wadda take
kai wa daf da ƙarshe a wasa 14 daga 16 da ta halarta, wadda ta lashe kofin karo
uku jumulla.
Masar za ta buga Afcon a Kamaru karo na 25 tana gaba a halartar
wasannin, kuma ita ce ta ɗaya a lashe kofin mai bakwai jumulla.
Tun lokacin da Mohamed Salah ya fara buga Afcon a gasar 2017, yana da
hannun a cin kwallo kaso 60 cikin 100, wato ya ci huɗu ya bayar da biyu aka
zura a raga daga 10 da tawagar ta ci.
Rabon da Masar ta ɗauki kofin nahiyar Afirka tun bayan gasa biyar,
wato tun bayan da ta lashe kofi uku a jere a 2006 da 2008 da kuma 2010 daga nan
shiru kake ji.
A ya yi wasan tsakanin Najeriya da Egypt Mohamed Salah ya taka rawar gani soasai a daidai
lokacin da Super Eagles ta
Najeriya ta buɗe gasar cin kofin nahiyar Afirka da ci 1-0 a gasar.
Bayan tashi daga wasan shahararren ɗan wasa Mohammed Salah ya sa
kai ya fita daga filin wasan.
0 Comments