Talla

Nafisa Abdullahi: Tauraruwar Kannywood ta janye daga shirin 'Labarina'

Daga: Hauwa’u Bello

02 Janairu, 2022

ABUJA, NIJERIYA — Tauraruwar wadda ita ce babbar Jaruma a cikin fim ɗin ‘Labarina’ fim mai dogon zango wanda ya ja ra’ayin al’umma ta sanar da cewa za ta bar fitowa a cikin fim ɗin saboda wasu dalilai na raɗin kanta. Nafisa ta sanar da haka ne a wata doguwar takarda data rubuta da kamfanin dake shirya fim ɗin wato Saira Movie daga bisani kuma ta faɗi haka a shafinta na Instagram inda ake da mabiya masu ɗinbin yawa.

Kodayake, wasu na yaɗa jita-jitar cewa ta bar shirin fim ɗin ne saboda rashin jituwa da suka samo da shugaban Kamfanin Saira Movie.  Amma har yanzu babu wani ko wata da suka tabbatar da wannan labarin na shaci-faɗi.

Nafisa Abdullahi ta taka muhimmiyar rawa a cikin shirin inda ta ja ragamar shirin a matsayin babbar tauraruwa, ta fito da sunan Sumayya, a cikin fim ɗin ‘Labarina’ an nuna Sumayya a matsayin ɗiyar talakawa wadda take zaune da mahaifiyarta, mai kamun kai da neman na kanta, ɗaliba da take faɗi-tashi don nemar wa kanta inganacciyar rayuwa.

Ga dai abinda ta rubuta a shafinta na Instagram inda take da ɗimbin mabiya:

Happy New Year to you all

‘Labarina’ Project ne da nake alfahari da shi ah duk inda na shiga. Saira Moɓies is also like my own company because mun Jima Muna aiki tare. I’m ɓery sad to let you all know bazan ci gaba da Aikin ‘Labarina’ ba, dalili shine rashin samun lokaci na yadda ya kamata, i haɓe my own businesses, school, a company to run and also my own films that I’m planning to start shooting ɓery soon. Bazan ce ah jira ni sai sanda na samu lokaci ba, dole za’a ci gaba da film din ‘Labarina’ ko da ni ko ba ni.

 

Ina ba dubban masoya hakuri Akan fita ta daga shirin. Alakata da Saira Movies Zata ci gaba da tafiya lafiya, babu hayaniya ko cin zarafi, Allah Kuma ya basu sa’a Wajen kammala sauran shirin.

— Nafisat Abdullahi.

Jim kaɗan bayan ta wallafa wannan rubutu, mabiyanta sun fara nuna takaicinsu a kan wannan mataki da ta ɗauka, ga abinda wasu ɗaiɗaikun mabiyanta suke cewa,

bab_jauro ya ce, “Mu dai gaskiya bamu ji dadi ba”

Ita kuma haphsertidreess cewa ta yi, “Eyyah😢 but I'm so happy for you😍Allah y taimaka ya kara daukaka. Allah yasa kifi haka. Amin”

Shi kuma skasim_abubakar_iya cewa ya yi, “Allah ya bada sa'a Allah ya sa haka shi ne mafi alkhairi amen”

A cikin abinda ta bayyana, fitarta daga cikin shirin ‘Labarina’ ya biyo bayan yawan ayyukanta da kasuwancin data sa a gaba da kuma fim ɗinta da zata fara shiryawa nan gaba kaɗan. Saidai fitarta ya zama wani abun tsaiko ga shirin inda dama can masu kallo suka ƙagara suka makomar Sumayya a cikin fim ɗin, wadda aka yi kidnafin. Duk da yake dai saurayinta Presidor ya ɗauki tawagar ‘yansa kai sun je maɓoyar da aka ɓoye Sumayya, saidai kafin su kuɓutar da ita sai ɓarayin suka kuna wa gidan wuta. Masu kallo za su so su ji, ko akwai Sumayya cikin waɗanda suka ƙone bayan banka wa gidan wuta?


Post a Comment

0 Comments