Labarin Danliti Sullutu
Daga: Littafin Hikimarka Jarinka na Bello
Hamisu Ida
Sullutu shi ne sunan da aka fi saninsa da shi. Ana
kiransa da wannan sunan don ya cika wauta, duk garin babu mai wautarsa.
Iyayensa babu abin da ba su yi ba don dai ya rage wauta amma a banza
wai man kare. Har makarantar allo an kai shi
garin Funtuwa wautarsa ta sa aka maido sa gida.
Wata rana
Sullutu yana barci cikin zauren gidansu ya kima babbar riga da zungureriyar
hularsa, sanyin zaure ya daki jikinsa yana munshari yana shura ƙafa.
Ya saki wani murmushi a bayyane sannan ya juya
kwanciyarsa gami da ƙara rumtse idanuwansa.
Ya yi rashin sa’a, wata Akuya
da tawagarta ta shararo da gudu, wasu suka tunkari
shimfiɗarsa wasu suka nufi cikin gida da gudu, babu shiri ya tashi da ga
barcinsa. Ya saɓe babbar rigarsa zungureriyar hularsa na kallon soron gidansu,
ya yi tagumi yana kallon Awakan suna shiga gida, duk zuciyarsa ta yi ƙunci.
Abin da ya faɗo masa a zuciya shi ne samɓaleliyar Budurwar da ya haɗu da ita a cikin mafarki. In zai iya tunawa ta ce masa tana zaune a birnin Zariya.
Baƙin ciki ya addabe sa, ya kulle kayansa sai
birnin Zariya neman budurwarsa ta mafarki.
Ya kama hanya, tafe yake baki buɗe yana kallon
manyan gine-gine da motoci, babura da kekuna har ya kawo ƙofar wani babban
gida.
Ya nemi waje ya zauna, bakinsa buɗe yana kallon
gidan, wata zungureriyar mota ta fito daga gidan, tayi gabas, bayan awa biyar
motar ta dawo, har lokacin Sullutu na nan zaune yana hammar yunwa.
Motar ta tsaya, shi kuwa Sullutu sai kyarma ta
gwace masa, Alhaji wanda aka fi sani da Mai Buhun Naira ya fito sannan ya kalli
Sullutu tausayinsa ya kama shi, ga alama zai iya yin gadi.
Daga nan Mai Buhun Naira ya ɗauki Sullutu gadi,
kullum yana bakin ƙofa yana shan inuwar silin. Ashe Sarkin gidan Mai Buhun
Naira ya ji haushin zuwan Sullutu kuma yana da kulalliya cikin zuciyarsa.
Wata rana Mai Buhun Naira ya yi tafiya, sai Sarkin
gida ya kira Sullutu ya bashi kayan wankin Mai Buhun Naira ya ce ya je ya kai
su can cikin ɗakin Mai Buhun Naira.
Ɗakin ko matan Mai Buhun Naira basa shiga saboda
duk wata dukiya tashi tana cikin wannan ɗakin. Sullutu ya ɗauki kaya ya shiga
cikin gida.
Matan Mai Buhun Naira suka ji motsi, su duba sai
ga mutum cikin ɗakin Mai Buhun Naira, suka yi ihu ɓarawo, aka kama Sullutu, nan
da nan aka kira ‘yan doka aka ɗaure Sullutu sai ofishin ‘yan doka.
Mai Buhun Naira ya dawo aka bincika, ashe duk an
wawushe ɗakin Mai Buhun Naira, an ɗauki maƙudan kuɗi. Aka tsananta bincike amma
Sullutu bai fito da kuɗin da aka sata ba, ‘yan doka suka shiga jibgar Sullutu.
Da wahala ta tsananta ga sullutu sai wata dabara
ta faɗo masa, ya shiga murɗe-murɗe yana gaza cikinsa na ciwo, ya faɗi ƙasa yana
ihu har aka ji shi, aka garzayo aka ɗauke shi sai asibiti, daidai za a shiga
mota da shi, sai ya sulalo ya faɗo ƙasa ya warware, ya ranta a na kare. ‘Yan
doka suka rufa masa baya, abinka da baƙauye ya yi masu fintikau.
Ya rinƙa shiga lunguna, har Allah ya maido shi wajen
da ya fara tsayawa, watau kusa da gidan Mai Buhun Naira, ya samu waje ya rakuɓe,
can wata budurwa ta fito daga gidan Mai Buhun Naira, gaban Sullutu ya faɗi, ya
tuna budurwarsa ta cikin mafarki, cikin sauri ya isa gabanta ya ɗuka har ƙasa.
Kallo ɗaya ta shaida Sullutu, shi ne wanda Sarkin
gida ya ja wa sharrin Sata, budurwar ɗaya ce daga cikin masu yin wanke-wanke
gidan Mai Buhun Naira, amma Sullutu bai santa ba.
Sullutu Ya roƙe ta ta ɓoye shi, ta ja shi zuwa
wani gida, ya kwashe duk abin da ya faru
ya gaya mata. Ta ce masa Sarkin gida ne ya haɗa kai da wasu ɓarayi, bayan an
kira ‘yan doka ɓarayin suka yi amfani da wannan damar suka shiga ɗakin Mai
Buhun Naira suka wawushe dukiya.
Sullutu ya tambaye ta ko ta san inda zai ga ɓarayin?
Ta ce masa a’a amma zata taimake shi su kama Sarkin Gida, ta bar Sullutu nan ta
koma gidan Mai Buhun Naira, tana shiga Sarkin Gida ya ce ta kawo masa abinci,
ita kuwa ta fakaici ido ta sanya masa banju cikin abinci, yana ci barci ya ɗebe
sa, ta mirgina shi ta sanya cikin buhu, ta ciciɓe sa ta aza bisa baro ta tura
sai gidan da Sullutu ya ke, suka ɗaure sa tamau.
Wasu Labarai
- Labarin Jatau Mawaƙi
- Labarin Akuya mai Magana
- Labarin Ƙaiƙayi Koma Kan Masheƙiya
- Labarin Na Shiga Ban Ɗauka Ba
- Labarin Sarkin Dawa
- Labarin Aikata Alheri Duk Inda Ka ke
- Labarin Ka So Naka, Duniya Taƙi Sa
- Labarin Ɓarawon Birni Da na Ƙauye
Bayan ya farfaɗo Sullutu ya shiga jibgarsa, ita
kuwa Budurwa ta nufi caji Ofis. Sai ga ‘yan doka, aka kama Sarkin Gida da
Sullutu sai ofis. Sarkin Gida ya ji matsa ya faɗi gaskiya, shi ne ya haɗa kai
da ɓarayi aka sace dukiyar Mai Buhun Naira, aka kama ɓarayin ɗaya bayan ɗaya.
Aka gurfanar da su gaban kuliya. Alƙali ya yanke
masu hukunci. Shi kuwa Sullutu ya kuɓuta. Har ya kama hanyar ƙauyensu, Mai
Buhun Naira ya sa aka kira shi ya damƙa masa kyautar kuɗi masu ɗimbin yawa.
Sullutu ya koma gidan su wannan budurwa suka
daidaita aka ɗaura masu aure, Mafarkinsa ya zama gaskiya.
Ya koma gida, ya ci gaba da noma, duk ƙauyen babu
matashi mai kuɗinsa.
0 Comments