Biyar ga
watan Agusta, Shekara ta Dubu Biyu da Ashirin
Ya cire
takalmasa, ya ɗora tafin ƙafarsa bisa ƙasa don nuna girmamawa ga ƙasarsar
mahaifarsa. Ko da ya ƙura wa ƙasar ido, ya fara tuna wasu abubuwa, musamman a
wata rana, a wannan gari, a yanayin damuna.
Duk in damuna
ta sauka, aka samu ruwa mai ƙarfin gaske, a kan yi asarar rayuka, dukiyoyi da
fargabar rushewar gidaje. Ambaliyar ruwa na ɗaya daga cikin ibtila’in da ke
yawan samuwa a yankunan karkara da birane a Nijeriya.
Mazauna
yankunan dake gabar ƙorama sukan kwashe kayansu domin barin muhallinsu. Ya ci
gaba da tafiya har ya isa bakin wani kango dake jingine da ƙorama wanda ruwa ya
zaizaye har ya koma kufai. Akwai gidaje fiye da hamsin da suka koma kufai. Nan
ne kakarsa ta raine shi, faifan abubuwan da suka faru ya dawo masa sabo, a wata
rana ne.
Baba Marwa na
zaune ƙofar gidanta inda take sayarda ɗanwake, Gab da faɗuwar rana, gari ya yi
lullumi, ga alama wani abu ne ya rufe sararin samaniya, yanayin bashi da kyau
sosai. Rassan itace suna kaɗawa, akwai iskar hadari, akwai kuma gizagizai wanda
ke tafiya yana haɗewa da wani irin baƙin hadari, aka fara iska mai ƙarfin gudu
da gawurtacciyar guguwa.
Cikin azama
ta kashe wutar ɗanwaken, sannan ta tattara kayanta, jikokinta Musa da Hassatu
da kuma autarta mai suna Karima suka ɗauke kayan suka shigar da su gida. Koda
ta shiga cikin gidan sai ta ɗaure tumakin da take kiwo a garkensu. Musa na da ƙarancin
shekaru amma ya hasashi faruwar wani abu, cikin tsoro ya ce mata,
“Babarmu mu
fita mu bar gidan nan, kar ayi ambaliya, kin ga bayan ƙorama gidanmu yake”
Da katse shi,
cikin faɗa irin na tsaffi ta ce,
“Har iyayenka
nan suka girma, babu abinda ya taɓa faru”
Ta tasa ƙeyar yaran suka shiga ɗaki suka rufe domin gujewa wa
ruwan saman da ya fara sauka.
Aka yi walƙiya
mai ƙarfi haɗe nau’in lantarki, ruwa mai ƙarfi ya fara sauka haɗe da tsawa,
cikin tsoro baba Marya ta ce da Karima watau autarta,
“Ku hau saman
gado”
Za a iya
fahimtar tsananin tsoro a idanuwan yaran, autar ta ce, “Inna ko fita za mu yi
kar ginin ƙasa ya faɗo mana”
Cikin tsoro
Baba Marwa ta ce,
“Shekara da
shekaru muna zaune bayan ƙorama, babu abunda zai faru” Cikin fargaba suka ci
gaba da addu’a, zukatansu na bugawa a daidai lokacin
da ruwa mai ƙarfi
ke bugun saman kwanon gidansu, a hankali ruwan ya fara cika tsakar gida, yana
ambaliya cikin ɗakuna, ruwan ya riga zaizayar ƙasar da aka gina gidajen
unguwar, yana nemar hanya don komawa cikin ƙorama.
Ruwa ya shiga
ɗakin Baba Marwa, har ya kama daidai guiwa, ta sauko daga saman ɗanbono, sannan
ya rirriƙe hannayen jikokinta da autarta, ta buɗe ƙofar ɗakin suka fito waje.
Ko kafin su fito ruwa ya cika ɗakin, wani ɓangare na bangon gidan ya rufta,
ruwan ya bi ta gefen bango ya yi hanya, yana komawa cikin ƙoramar dake bayan
gidajensu.
Ƙarfin ruwa
da iska suka ja Musa, ya faɗi ƙasa, kansa ya bigi gefen ƙasa, ruwa ya ja shi ta
cikin ramin da ruwa ya yi, ya faɗa cikin ƙoramar, jikinsa ya bugi duwatsun ƙorama.
Baba Marya na
riƙe da hannun ɗiyarta da jikarta, har ruwan ya ci ƙarfinsu sannan ya ja su
zuwa cikin ƙorama. Koda ta buɗe baki ta niyar faɗar,
“Wayyo Allah
na”
Sai ruwa ya
cika bakinta, ta gunshe ruwan ta haɗiye. Ba ta san lokacin da ta saki hannayen
jikar da autarta ba. Su ka ci gaba da iyo suna ƙumtsar ruwa ta baki ta hanci.
Ba gidan Baba Marwa kaɗai ne ya rushe ba, akwai gidaje fiye da ɗari
biyar da suke jingine da ƙoramar, wasu bangaye sun zube, wasu iska ya ɗauke
kwanon gidaje, wasu kuwa ruwa ya cika gidajen ta yadda magidanta suka rasa
hanyar fita.
Bayan
manya-manyan duwatsu, da tsaunuka, da jeji, da filaye da muke da su a duniya,
har wa yau duniya ta ƙunshi manya-manyan ruwaye da suka haɗa da tabkuna da
rafuka, da gulabe, da koguna da tekuna. Ƙasar da ke shimfide ba a shafe take
ba, tana da tudu da kwari da rami da kwazazzabai . Abu ne mai wahala a iya yin
amfani da kimiyyar gine-gine domin samun ingantaccen muhalli.
Musa dake
tsaye gaban kangon gidansu ya yi amanna da cewa, ana iya kare ambaliyar ruwa
idan aka yi tsare-tsaren da za su inganta muhalli musamman a yankunan da suke
makwabtaka da ƙoramu da tabkuna da rafuka da gulabe da koguna ko tekuna.
Musa ya ci
gaba da zagayawa yana nazarin yadda zai iya tsara ingantaciyyar hanyar ruwa a
tsohuwar unguwarsu. Shugaban bankin bayar da bashi don inganta muhalli ne ya
taswirar yankin. Kafarsa babu ko takalmi, ya kan taka caɓali da taɓo da jiƙaƙar
ƙasa da ta rufe hanya, akwai tsirai da ciyawa da bola da suka cika gefe-gefen
unguwarsu.
Zuciyarsa ƙuntace,
yana kallon zubi da tsarin tsohuwar unguwarsu, ba kamar unguwar da yake zaune a
yanzu ba wacce bankin ba da lamunin kudi don yin ingantaccen gini ta gina
sannan ta ba su bashi da rahusa mai sauƙi.
Ko bayan ya
zagaya cikin duniya, ya fahimci hanyoyin da za su iya magance ibtila’in ambaliyar
ruwa da ya addabi yankinsu. Idan za a samar da magudanar ruwa a cikin
unguwanni, da kwashe bola a duk inda aka tara ta, da fitar da hanyoyin ruwa a
cikin birane da karkara, da yin shuke-shuken itatuwa da za su taimaka wajen riƙe
ƙasa da ƙara mata ƙwari, to lallai za a samu ingantaccen muhalli.
Musa ya yi hasashen cewa, a damunar bana, a wannan wata na
Agusta, in dai ba ayi ingantattun madatsun ruwa ba, to akwai jihohi da yankuna
a Nijeriya inda za a iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwa, sanadiyar ruwan
sama da kuma cika da batsewar tafkunan dake a cikin ƙasar.
Wasu Labarai:
0 Comments