Talla

Mutum 19 Sun Mutu A Wani Haɗarin Mota A Kano

Daga: Hauwa’u Bello

07 Janairu, 2022

ABUJA, NIJERIYA - An samu wani haɗari a kan hanyar Kano zuwa Zaria, inda mutane 19 suka rasa rayukansu, haka kuma, ƙarin mutum 26 suna asibiti. Haɗarin ya faru ne a ranar alhamis kusa da Makarantar Horar Da Aikin Lauya da ke Bagauda a Jihar. Motoci ƙirar bas-bas ne suka yi taho-mu-gama wanda ya yi sanadiyar kamawarsu da wuta. Dukkan bas-bas ɗin motocin hayane, saboda gudun da direbobin suke yi ne yasa suka kasa sarrafa motocinsu, wasu daga cikin direbobin sun ƙone, wasu sun rasa rayukasu wasu kuma an ɗauke su zuwa asibiti don karɓar taimakon gaggawa.

An ji ta bakin jami’in hulɗa da jama’a da wayar da kai na hukumar kare haɗurra ta Nijeriya reshen Jihar Kano, SRP Abdullahi Labaran yana cewa,

“Binciken da jami’anmu suka yi, sun gano cewa dukkan motocin biyu suna gudu ne sosai, kuma dukkansu motocin haya ne, gudun da suke yi ne yasa suka kasa sarrafa motocinsu”

Ya ƙara da cewa,

“Nan take motocin suka kama da wuta, wasu daga cikin fasinjojin ciki har da waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata sun ƙone, mun miƙa gawawwakin waɗanda suka mutu ga ‘yan uwansu, sauran aka kai su babban asibitin ƙaramar hukumar Kura dake Jihar domi karɓar magani”

Hukumar kiyaye haɗurra na bakin ƙoƙarinta wajen wayarwa mutane kai a kan yadda za su riƙa tafiya da ababen hawa, haka kuma suna bakin ƙoƙarinsu wajen ganin an rage haɗurra a Nijeriya, ta hanyar tilasta wa direbobin motocin haya da na gida sanya na’urar dake taƙaita gudun mota.

Hukumar bata tsaya a nan ba, tana shiga tashoshin motoci da ma’aikatun gwamnati inda ake jigilar mutane domin wayar masu da kai, haka kuma hukumar na tuntuɓar malaman addini don faɗakar da kan al’umma.

Haɗarin motoci dai ya zama ruwan dare a cikin ƙasar Nijeriya, inda ake samun rasa rayuka da kuma jikata. Duk da yake gwamnatin Nijeriya na bakin ƙoƙarinta wajen gyara tituna da gina sabbi amma al’umma na ɗora alhakin haɗurran saboda rashin kyawun tituna.

Post a Comment

0 Comments