12 Janairu, 2022
Daga: Suleiman Umar, Katsina City News
KATSINA, NAJERIYA - A wani taron manema labarai da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya kira makwanni biyu da suka gabata, an yi masa tambaya a kan zaɓen ƙananan Hukumomi a Katsina, inda ya ba da amsar cewa Gwamnatin Katsina za ta yi amfani da dokar Jiha ne wajen zaɓen, kuma za a yi zaɓen a kwatar farko ta shekarar da ake ciki ta 2022.
A kuma taron manema labaran da aka yi a Talata 11/1/2022, Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Jihar Katsina ta bayyana cewa, sun yi amfani da dokar zabe ta ƙasa, kuma sun ba da kwanaki 90 wanda zaɓen zai faɗa a kwata ta biyu ta shekarar 2022.
Binciken jaridun KATSINA CITY NEWS ta yi, Shugaban Hukumar Zaɓe ta Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Bako ne ya gamsar da Gwamnan a kan a kauce wa faɗawa rikicin kotu in aka yi amfani da dokar zaɓe ta Jiha wadda aka kafa tun zamanin tsohon Gwamnan Jihar, Ibrahim Shehu Shema na mulki.
Alhaji Ibrahim Bako ya gabatarwa da Gwamnan Katsina, wasu hukuncin babbar kotun ƙasa guda biyu da suka jaddada amfani da dokar Hukumar zaɓe ta ƙasa a wajen zaɓen ƙananan Hukumomi. Da kuma wasu hukunce-hukunce na soke zaɓe da aka yi a wasu Jihohi, waɗanda aka yi zaɓe da dokar Jiha, amma bayan an yi ƙara kotu ta rusa zaben.
An kuma gabatarwa da Gwamnan cewa Jihohi 24 da suka yi zaɓen ƙananan Hukumomi duk da dokar zabe ta ƙasa suka yi amfani.
A bisa waɗannan hujjojin Gwamnan ya ce, Kwamishinan Shari’a ya yi nazarinsu ya rubuto shawara, ya bi ya kuma ba da shawarar cewa;
“A zaɓen ƙananan Hukumomi na Jihar a yi amfani da dokar zaɓe ta ƙasa wadda ta bayar da kwanaki 90 domin gudanar da zaɓe.
Wannan shi ne ya sa Gwamnan Katsina ya canza shawara da kuma canza ranar zabe daga lokacin da ya shelanta a taron manema labarai zuwa ranar 11/4/2021, kamar yadda Hukumar Zaben ta Jiha ta tsara.
Wasu Rahotanni
0 Comments