Daga: Muhammad Abdallah
ABUJA, Najeriya - Masu iƙirarin jihadi
da ake zargin 'yan ƙungiyar ISWAP ne sun kashe mutum biyu sannan suka sace wasu
yara 20 a kusa da garin Chibok na Jihar Borno ranar Alhamis.
Wani shugaban yankin ya faɗa wa manema labarai cewa maharan sun
afka wa garin Piyemi, inda suka yi awon gaba da mata 13 da maza bakwai.
A cewar wani ganau, mayaƙan na Islamic State West Africa
Province (ISWAP) sun afka wa garin ne da rana cikin kakin sojoji suna
harbe-harbe tare da sace kayayyakin shaguna, sannan suka ƙona gidaje.
Wani mazaunin yankin mai suna Samson
Bulus ya ce,
"Sun harbe mutum biyu kuma suka sace yara mata 13 da maza
bakwai, shekarunsu zai kai 12 zuwa 15,"
Bayan sun sace kayan abinci sun xauke
yaran sannan suka sanya su cikin wata mota qirar akori-kura sannan suka shiga
daji da su.
Garuruwan Katsina, da Kaduna da Zamfara
da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren varayin daji masu satar mutane don
karvar kuxin fansa. Jihar Borno ta sha fama da hare-haren Boko Haram da ISWAP. Ko
a can baya an sha sace xalibai ana yin garkuwa dasu don karvar kuxin fansa.
- Buhari Ya Miƙa Ta'aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa Da Aka Kashe A Kano
- Wata Mata ta Kashe kanta a Kano
- An Sace Wani Basarake A Palato
0 Comments