Talla

Matasa Sune Jigon Kowace Siyasa

DAGA: Cmrd Abubakar Iliya.

Ba ƙaramin farin ciki na yi ba lokacin da ga irin yadda matasan mu suka bayyana haiƙan ta hanyar nuna sha'awar su a kan tsayawa takarar Kansiloli domin wakiltar mazaɓunsu a ƙarƙashin jam'iyyar PDP. Inda wasu kuma suke neman tsayawa takarar Ciyamomin ƙananan hukumominsu.

Hakan kuwa ya biyo baya ne tun daga ranar da Gwamnatin Jihar Katsina da Hukumar Zaɓe mai zaman kanta suka fitar da ranar da za a gudanar da zaben ƙananan hukumomi a jihar ta Katsina.

Tabbas abunda matasan mu suka yi ya tabbatar mana da cewa a shirye suke domin kawo sauyi a cikin Al'umma. Haka zalika ya nuna mana cewa matasan mu sun shirya domin kwatar 'yancinsu.

Duba da irin yadda ake amfani da matasa wajen samun kowace irin nasara a siyasar ƙasar nan amma sai a watsar dasu da zaran an samu nasara. To, wannan ne zai tabbatar mana da shin za a taimaki matasa a saka masu a kan irin ƙoƙarin da suke yi, ko kuwa dai kawai amfaninsu ake bukata ba ci gaban su ba?

Dan haka nake so nayi kira zuwa ga gwamnatin Jihar Katsina cewa ta gudanar da zaɓe na tsakani ga Allah. A bada dama kowa ya zaɓi wanda yake so, a kai akwatunan zaɓe dukkan mazaɓu. Rashin yib adalci a cikin wannan zaɓe zai iya zama barazana ga Dimokwaradiyyar Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

Sannan ina kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Katsina a kan ta gudanar da sahihin zaɓe na tsakani da Allah. 

Kira na karshe, shi ne a kan 'ya'yan jam'iyyarmu ta PDP. Mu kasance jajirtattu don tabbatar da nasarar 'yan takararmu, mu fito mu tsare kuru'un mu don kar ayi mana abunda ba daidai ba.

Daga ƙarshe ina yiwa duk wanda ya tsaya neman kowace irin kujera fatan alkairi. Allah ya shige mana gaba, ya yi mana jagoranci na alkairi.

Wasu Labarai:

  1. Wani Mahaifi Ya yiwa Ƴarsa ƴar Shekara 3 Fyaɗe
  2. Jarumar Fina-Finai Ta Zargi Kanta Da Ƙin Sake Yin Wani Aure
  3. Abin da nake Dubawa Kafin in Yarda a Sumbace ni a Fina-finai — Queeneth Agbor

Post a Comment

0 Comments