Talla

Littafin Makarantar Kwana Page 1

GABATARWA

Wannan littafin ƙirƙira ce, ban yi shi don wani ko wata ba, na yi shi ne a kan abinda ke faruwa a makarantar kwana a yanzu, Duk wanda ya karanta wani abinda ya sava tunaninsa ta yake gani kuskure daga kaifin alɗalamina, ina fata zai nusar da ni daidai da yadda za mu fahimci juna.

***

G G.C UNITY COLLEGE

MAKARANTAR KWANA, SWEERY | PAGE 1 Makaranta ce mai tarihi, tana ɗaya daga cikin manyan makarantun da ke cikin garin Bauchi kasancewar ita ce ɗaya tilo makarantar kwana wacce ta tara ɗalibai a gaba ɗaya yankunan Nijeriya, kama daga Arewa har Kudu. Makarantar ta tara ɗalibai da dama saboda irin karatun da ake yi da tsayawar da malamai suke yi don ganin sun samarwa ɗalibansu ilimi nagartacce.

A hankali ta buɗe idonta ta shaƙi iska mai ƙarfi, tsananin farin ciki ne ya kama zuciyarta saboda tsintar kanta a cikin makarantar. Kai tsaye wajen da ake ajiye motoci Abba ya shiga ya ajiye tasa motar. Buɗe motar ya yi, ya fito ita ma ta biyo bayansa, kai tsaye Admin Block suka je, ɗan abubuwan da ba a rasa ba aka yi, daga baya ya yi mata nasiha ya bata Pocket Money ya tafi. Sai a lokacin ta ji zuciyarta ta tsinke, Admin Officer ɗin ne ya sa aka kira masa wata Senior a cewar sa ita ce House Captain ɗinsu.

Sukayi musayar kallo, kodayake tun lokacin da Ummi ta ɗora idonta a kan na Deeja sai ta yi sauri ta sauke, can cikin zuciyarta tana ji kamar wani abu na shirin faruwa bayan rayuwar ƙunci da ta baro a baya.

"Deeja, ga Ummi nan a bata ɗaki a kuma sa ido a kanta".

"To Daddy" abinda ta faɗa kenan. Ta fita ta kira wasu, ga dukkan alamu Juniors ne irinta, kayanta suka ɗebe tamkar ƴan dako suka tafi har cikin Hostel ɗin, a nan ne ta san tabbas bariki iyawa ce, duk da kasancewar rana ce hakan bai hana idonta ganin abubuwa wanda suka kauce hanya ba, babu kunya bare tsoron Allah. Runtse idonta ta yi tana mai Allah wadarai da irin shigar banzan da wasu ɗalibai suke yi. A hankali zuciyarta ya fara tsananta bugawa da sauri da sauri.

House Captain Room shi ne abun da ta gani an rubuta a saman ɗakin da ta shiga, bin bayanta ta yi itama a hankali ta sauƙe ajiyar zuciya ganin ɗakin ba mutane sai gadaje guda biyu (bonk) waɗanda suka sha shimfiɗa. Hamdala ta shiga yi wa Allah don duk a tunaninta ta kauce ma faɗawa halaka irin na wasu ɗalibai data wuce ta gani a cikin Hostel.

Ajiye kayan suka yi suka fita, Sister Deeja ta ce,

"A nan za ki zauna sai ki shirya kayanki a can".

Tana gwada mata wajen ta fita. Zuba wa kayan ido ta yi tana karanta wasiƙar jaki.

Kasancewar yamma ta yi kuma Weekend ne kafin ta kammala jera kayanta ta fara jiyo hayaniyar waɗanda suka dawo daga Arabic Class, wata murya mai zaƙin sauraro ne ta daki dodon kunnenta.

Mai muryar ta ɗaga murya ta ce,

"Allahumma Rabbi Salli Allah, Salli Allah, Muhammadun shugaban gaskiya, Balarabe ɗan balarabiya, dominsa ne an kayo duniya, dominsa ne..." Bata kai ga ƙarasa maganar ba ta kutuntuma ashar.

"Kutumar jan uba! Wata tsinanniyar ce, mai bakin uwa, ƴar gidan taƙi zama, jikar ansalamar ce ta ɗauke mun net ɗina dana shanya?”

Ta ci gaba da cewa,

“Na rantse da Allah ko a dawo mani da shi ko nayi bura uba! Dan babu ‘ƴar iskar da zan ragarwa ‘yan kutumar...."

"Kai Zarah wai ke baki gajiya da danna ashar ne dan Allah? Yanzu fa ki ka gama ƙasida ko aya baki kai ba kin zo kina kutuntuma ashar kamar ‘ƴar gidan maguzawa".

"Hold on, nature"

Ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu.

Ta ci gaba da cewa,

"Ba ruwanki da Ni ina faɗa maki, ki daina shiga sabgata kin ƙi, to na rantse da Sarkin da yake busa mani numfashi zamu yi kutumar bura uba da ke, don ni ba ƙaramin abu ba ne a wajena na kwaɓe mu bugu".

"Ai daga magana sai nawa ya zama mai zafi?”

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce,

“Lallai kam! Ki sani ba da ni za kiyi ba don ni nasan me nake yi"

Tana gama maganarta ta wuce ta barta tana ta kumfar baki".

'Cabɗijam! Wai dama haka ake yi? Mutum ya yi ta kutuntuma ashar kamar bai san zafin iyayensa ba? Kai gaskiya wannan yarinyar bata da ɗabi'a mai kyau in dai haka take'

Ummi ke wannan zancen zucin fuskarta cike da al'ajabi gami da mamaki, bata taɓa zaton haka rayuwar makarantar take ba sai gashi a cikin mintuna ƙalilan ta fara karo da ɗabi'u maras sa kyau.

Bokitinta ta ɗauka ta fita waje da niyar zuwa deɓo ruwa don ɗaura alwalan sallah magriba da tayi, saboda a hanyar shigowarsu ta ga wani burtsi (borehole) a gaban Hostel ɗin, kanta a ƙasa take tafiya a hankali tamkar wacce ƙwai ya fashewa a ciki.

Ba tare da zato ko tsammani ba ta ji taci karo da mutum, wanda ya sata ɗagowa da sauri, kafin ta kai ga ganin wacce ta bige aka ɗauke ta wani irin azababben mari a fuskarta, wanda yasa ta jin sa tamkar sauƙar aradu.

"Don kutumar uwarki, ke makauniya ce da zaki buge ni?"

Maganar da tayi ne yasa Ummi kallonta, ga mamakinta sai ta ga gaba ɗaya mutanen da ke wajen suna darewa wasu har ƙasa suke tsugunnawa suna gaisheta kafin su wuce.

Bata kai ga bata amsa ba ta sake kife ga da wani wawan mari wanda yafi na ɗazu ƙara.

"Kutumar uwa wallahi ko ke kurma ce yau sai na ga uban da ya tsaya maki, don uban babanki".

Finciko ta tayi tamkar kayan wanki, ta yi hanyar Hostel dinsu da ita, tun daga nesa ka fara jin "Lallai yau lulu ta samu nama".

Zuciyar Ummi ce ta riƙa bugawa a take taji cikinta ya yi wani irin murɗawa.

Zan ci gaba….

Sweery

More comments more typing

Wasu Labaran Hikaya

  1. Makarantar Kwana Page 1
  2. Gaba Kura... Page 1

Post a Comment

4 Comments

  1. Da kyau abu ya yi Allah ya saka da alkhairi

    ReplyDelete
  2. Sannunku da kokari, wannan labari ya ja hankali, Allah ya kara basira

    ReplyDelete
  3. Muna fatan ci gaba da jin yadda labarin zainkasance

    ReplyDelete
  4. Masha Allah,Allah Ya ƙara basira

    ReplyDelete
Emoji
(y)
:)
:(
hihi
:-)
:D
=D
:-d
;(
;-(
@-)
:P
:o
:>)
(o)
:p
(p)
:-s
(m)
8-)
:-t
:-b
b-(
:-#
=p~
x-)
(k)