Talla

Labarin Kaikayi Koma Kan Mashekiya

Labarin Wani Matashi Da Ya Koma Jaki

Daga: Littafin Hikimarka Jarinka na Bello Hamisu Ida

Daɗaɗɗen labari da ya rutso zamanin Barbushe shugaban masu bautar gunki tsunburbura dake zaune a Dutsin Dala na Kano.

A wannan zamani duk shahararka ba komai ba ne sai ka haɗa da tsafi, don haka tsafi ya zama ruwan dare.

Akwai wani Boka da ya zo wannan yanki, bokancinsa ba na cutar kowa ba ne. Ya zo neman dukiya, mahaifinsa ya aiko sa tare da ƙaninsa su ɗebe wata dukiya da take tsube cikin wasu koguna dake saman Dutsin Dala, dukiya tsantsar zinari da tagulla.

Wannan ne ya sa Boka Guguwa zuwa Kano tare da ƙaninsa mai suna Nazaki, ya zauna kusa da gidan Boka Danburu mai gida a Gwauron Dutsi daga gabashin Kano, Boka Danburu ɗaya ne daga cikin fadawan Barbushe.

Boka Guguwa ba ya ƙaunar Nazaki, Ƙaninsa ne ubansu ɗaya, mahaifinsa yana tsananin ƙaunar Nazaki saboda kyawawan halayarsa, don ƙaunar da yake wa Nazaki ya yi alƙawarin zai mallaka masa kayan tsafinsa.

Ubansu wani shahararren matsafi ne, wajensa Boka Guguwa ya koyi harkar tsafi, ya na baƙin ciki da kayan tsafi da za a ba ƙanensa, don haka ne ma ya shirya tahowa da shi neman dukiya, don ya halaka shi.

Boka Guguwa ya gama duk shirye-shiryensa na shiga Kogon Dutsen Dala sai ya kira Nazaki ya ce masa,

“Zan aike ka Dutsen Dala, amma fa ba na son kuskure ko wauta.”

Ya ɗauko guru da laya tare da masakkai ya ba Nazaki ya ce,

“In tsakar dare ya yi sai ka tafi Ƙofar Dawanau ka rumtse idanuwanka sannan ka kira sunan mahaifinmu sau uku ka shafi wannan gurun, gurun zai kai ka cikin Kogon Dutsen Dala inda dukiya ke tsibe, ka yi sauri ka cika mani waɗannan masakkai da zinariya da tagulla. Da zaran ka cika ka ɗora wannan laya saman masaki ka sake kiran sunan babanmu. Ha! Ha!!Ha!!!” Boka Guguwa ya ɓarke da dariyar ƙeta.

Kullum addu’ar Nazaki Allah ya fitar da shi daga sharrin boka Guguwa. Ya san ba ya da wani farin-ciki face ya ga ya halaka shi. Da dare ya tsala Nazaki ya kama hanyar Ƙofar Dawanau yana ta Addu’o’i, yana isa bakin ƙofar ya ci karo da wani saurayi, ya roƙe shi arziki ya haye da shi saman Dutse yana son kai gaisuwa wajen gawar Barbushe.

Nazaki yaro ne mai son taimakon duk wanda ya nemi taimakonsa. Ya kama hannun saurayi ya shafi guru, suka ɓacce sai Kogon Dutsen Dala mai ɗimbin dukiya. Ashe wannan saurayi Boka Guguwa ya turo shi don ya sace gurun da zai mai da Nazaki gida, ya kasa saukowa dodanni su cinye shi.

Bayan Nazaki ya cika masakkai da dukiya kamar yadda Boka Guguwa ya umurce sa ya aza laya saman masakkai ya kira sunan babansu, take masakkai suka ɓace. Bai ankara ba saurayi ya busa masa wani baƙin hayaƙi, ya faɗi ƙasa sumamme. Kafin ya farfaɗo saurayi ya ɗauke gurun ya shafa ya ɓace, ya bar Nazaki nan.

Lokacin da ya farfaɗo sai ya fahimci abin da ya faru, ya kuma sakankance da makircin yayansa ne Boka Guguwa. Ya ɗaga kai ya gaya wa Allah, yana cikin Addu’a sai ga wasu Dodanni, Nazaki ya sake yin lamo kamar ya suma, suna zuwa suka ɗauke sa bisa kafaɗa suna gurnani tare da wata irin jagwalwalon magana, kamar suna cewa,

“Sarauniyar Dodanni ta samu abin kalaci”.

Su ka jefa shi cikin wani kogo, kafin gari ya waye. Nazaki ya tashi ya gansa cikin wannan kogo ga tarin gawarwaki, ya ga wani rataye da guru irin nasa, cikin sauri ya rubace gurun ya shafa, sai ga shi cikin wata ƙawatacciyar fada, tasha ado, ga kujerun zinari nan birjik, an yi wata fafaɗar shimfiɗa an jera abinci kala-kala, iyakar ganinsa bai ga ƙarshen abincin ba.

Cikinsa ya yi gurnani, ya tuna yunwar da yake ji, cikin sauri ya isa ga shimfiɗar abincin ya kai wa wani akushi da ke ta ƙamshi cafka ya cinye abincin dake ciki. Yana gama cin abincin cikinsa ya murɗa, kunnuwansa suka ƙara tsawo, jikinsa ya rinƙa fitar da wani irin gashi, ƙafafuwansa suka koma kofato, a hankali sifarsa ta fara canzawa har ya koma jaki, Nazaki ya yi Kabbara sannan ya kai wa wani akushi Cafka da bakinsa ya lamushe abincin dake cikinsa, a hankali ya sake komawa sifarsa ta asali. Ya yi murmushi sannan ya ɗebi wannan abinci da ya fara ci, ya sake shafa gurunsa. Cikin hukuncin Rabbana sai ga shi cikin ganuwar Kano kusa da Gwauron Dutse.

Ya samu shuni ya shafe duk illahirin jikinsa, ya ɗauko ƙoƙon bara ya shiga gidan da Boka Guguwa yake. A daidai lokacin yana ɗakin tsafinsa, wannan Saurayi da ya yaudare shi yana dafa abinci, shi ne yaron Boka Guguwa mai yi masa hidima. Nazaki ya shammace sa ya zuba abincin da ya ɗebo wanda ke rikiɗar da mutum ya koma sifar jaki cikin abincin da ya ke dafawa, sannan ya ficewarsa. Ya samu waje bayan gidan ya laɓe.

Wasu Labarai

  1. Labarin Jatau Mawaƙi
  2. Labarin Akuya mai Magana
  3. Labarin Ƙaiƙayi Koma Kan Masheƙiya
  4. Labarin Na Shiga Ban Ɗauka Ba
  5. Labarin Sarkin Dawa
  6. Labarin Aikata Alheri Duk Inda Ka ke
  7. Labarin Ka So Naka, Duniya Taƙi Sa
  8. Labarin Ɓarawon Birni Da na Ƙauye

Yaro na gama dafa abinci ya ɗiba ya kai wa boka nasa can ɗakin tsafinsa, sannan ya tsugunna ya lashe nasa. Shi ma boka na fitowa daga ɗakin Sihirinsa ya cinye duk abincinsa.

Cikin Boka Guguwa ya murɗa, kunnuwansa suka fara ƙara tsawo, Ƙafafuwansa suka koma kofato.

 Kafin ya ɗauki wani mataki har sifar jikinsa ta koma jaki, shi kuwa wannan Saurayi ya koma jakanya. Nazaki dake laɓe ya fito ya kama jakuna ya kai kasuwa ya sayar ya dawo gidan Guguwa ya kwashe duk dukiyar da ya ɗebo cikin Kogo sannan ya kama hanyar Katsina, inda ya ci karensa ba babbaka. An ce wannan shi ne farkon fara yin kasuwancin jakai a Kano. Yanzu haka in ka je kasuwar Kurmi za ka ga ana ta hada-hadar kasuwancin Jakai.

 

Post a Comment

0 Comments