Yadda Jatau ya Yaudari Tsuntsaye
Jatau mutum ne mai biyayya in yana son wani abu daga gare ka, yakan rinƙa biyayya sau-da-ƙafa har sai ya cimma burinsa. Tsafi shi ne gadon gidansu, kakarsa ita ce Sarauniyar Bori, Duk lokacin da aka tashi yin bikin Shan Kabewa.
Sarauniyar Bori watau kakar Jatau ita ke hawa saman turmi ta hau wata tsohuwar kuka dake ƙofar gidansu wace ta girmi kakanta ta dirko bisa kabewa. Aikin Jatau a wannan rana ta shan kabewa shi ne riƙe wa kakarsa jakar tsafinta, har sai ta farfaɗo daga bori, watau har sai Inna Uwa ta sauka.
Bayan kakar Jatau ta mutu sai aka ba mahaifiyarsa gadon Sarautar bori ta kasance Sarauniyar Girka. Haka dai Jatau ya tashi tsakanin matsafa har ya ƙware cikin harkar tsafi.
Duniya babu abin da Jatau yake so illa waƙa, yana so ya ji yana rera waƙoƙi irin na mawaƙan gargajiya na Hausa. Yakan shirya ya yi ’yan tsubbace-tsubbacensa ya tara mutane ya buɗe baki yana ƙaraji wai shi a dole waƙa yake rerawa.
Da ya fara rurinsa ɗai-ɗaya da ɗai-ɗaya mutane kan tsere su bar Jatau. Shi kuwa ya taƙarƙare yana warar baki har sai ya gaji. Abin da ya kasa fahimta shi ne, ita waƙa baiwace.
Duk lokacin da Jatau ya ci tuwo ya ƙoshi ya kan ɗauki gurmi ko ganga ya tafi Dandali yin waƙa, da mutane sun hango shi sai su yi ta kansu su gudu. Wannan abu kuwa yana masa ciwo.
Wata rana Sarauniyar Girka ta aiki
Jatau daji ya ɗebo
mata wasu saƙe-saƙin itatuwa tare da kaucin damo da
kuma saɓar maciji,
ta umurce shi ya samo mata ƙwan makwarwa.
Ta fara shirya bikin da ya gabato na shekara watau bikin Shan Kabewa, ta yi wa ɗanta alƙawari za ta yi masa baiwar waƙa a ranar biki in dai ya samo
mata abin da ta buƙata.
Jatau ya ɗauki kayan farauta ya shiga jeji don cika umurnin Sarauniyar Bori, ba shi da wani buri sai ta yi masa baiwa a cikin harkar waƙa.
Shi ne har dajin rugu na ƙasar Sakwato, duk sai da ya gama samo abubuwan da Uwar-Girka ta umurce sa, amma ƙwan makwarwa ya gagara, makwarwar kanta ta gagari ya gan ta. Kwanansa uku yana nemanta bai samu ba.
Rannan yana zaune ƙarƙashin wata tsamiya yana hira da mutan ɓoye, sai wata dubara ta faɗo masa. Nan-da-nan ya buɗe jakar tsafinsa, ya ɗebo wani garin magani ya barbaɗe jikinsa da shi, ya sake ɗebo wasu ruwa cikin duma ya fitsare sa ya kurɓe ruwan, ya kurma ihu ya kalli Yamma yana wasu surutai yana cewa, “Jikan Sarauniyar Bori nake ɗan Sarauniyar Bori, Uwar-Girka ta aikoni, ko aiken ya gagara? Sammani fifike na jaraba tashi ko na dace.”
Yana gama sabbatu sai ya rikiɗa ya zama mujiya. Mujiyar ta lula cikin itatuwa tana neman dabar tsuntsaye. Tana cikin lulawa cikin sararin samaniya sai ta hango dabar tsuntsaye, cikin sauri ta sauko cikinsu, tana zuwa ya laɓe nesa da su bisa wata itaciya, tana kallon yadda suke gudanar da rayuwarsu, har tsawon kwana uku.
Duk in safiya ta yi kowace tsuntsuwa sai ta tafi neman abinci, in uwa ce ta samo wa ‘ya’yanta ta kawo masu, uwa kuwa mai ‘ya’ya ‘yan dagwai-dagwai takan ɗauke su ɗaya-bayan-ɗaya ta rinƙa koya masu tashi, da ƙarami ya nufi abin cutarwa sai babbar tsuntsuwa ta sha gabansa tana tsuwwa alamar gargaɗi.
In marece ya yi duk tsuntsaye za su taru waje ɗaya kowa ya rinƙa rera waƙoƙi irin wacce ya iya da muryoyi masu daɗin saurare.
Mujiya dai tana sauraren muryoyin tsuntsayen abin na burgeta, wasu lokutan har kuka take yi, don baƙin cikin ba ta da murya mai daɗi irin ta su, ba za ta yi ƙasa a guiwa ba, bayan ta samu ƙwan makwarwa tana buƙatar ta zambaci tsuntsaye.
Ga dai tsuntsaye nan kala-kala irinsu, Aku, tantabara, ɗawisu, moli-moli, kurciya, kazar-daji, kanari, shaho. Aku shi ne Sarkin dabar tsuntsaye. Kowane tsuntsu da irin tasa rayuwar daban, amma babu wanda ya damu da rayuwar ɗan’uwansa.
A kwana na huɗu Mujiya ta bari sai da tsuntsaye
suka taru ana ta kai wa Sarki Aku gaisuwa, sai ta shiga cikin dabar, ta isa
gaban Sarki Aku ta faɗi ta
yi gaisuwa tana kuka, sannan ta ce, “Da girman kujerarka, ina neman taimako.”
Aku ya kalli mujiya sama da ƙasa ya gama karantarta sannan ya
ce, “Ina jin ki, ko da yake da ganin ke ba ‘yar asalin dabarmu ba ce”.
Mujiya ta ce, “Lalle kam, ni ba ‘yar
asalin dabarku ba ce, Allah ya ba ni wata fasaha ta mai da fari baƙi, sannan in mayar da mummuna kyakykyawa,
wannan ne ya sa aka yi mani zagon ƙasa
a dabarmu shi kuwa sarkinmu ba ya da adalci sai ya kore ni, ina neman alfarma
in zauna cikinku har in samu wajen zama in koma.”
Aku ya yi murmushi ya ce, “Za mu ba ki
amana iyakar abin da Allah ya hore mu da shi, da fatan za ki riƙe alkawari ba za ki cutar da mu
ba.”
Mujiya ta yi alƙawari ba za ta cutar da kowa ba, nan ta shiga cikin tsuntsaye ta ci gaba da hidimominta, duk inda ta gilma sai sauran tsuntsaye su saki baki suna kallon kyakyawan gashin jikinta wanda ke da kaloli masu kyau, wani ɓangare, fari, wani baƙi, wani ɗorowa-ɗorowa, wani ɓangare kuma ja-ja, wani kore, wani ko makuba, wani ɓangaren gashinta kuwa wankan tarwaɗa ne.
Wannan abu shi ya rinƙa burge su, suka rinƙa roƙon mujiya ta ara masu gashinta, amma sai ta ƙi, duk lokacin da aka tashi rera waƙoƙi sai ta noƙe ta yi ƙarya ta ce mura take yi.
Rannan dai tsuntsaye suka taru suka je wajen Sarki Aku ya taimake su ya tursasa Mujiya ta ara masu gashinta su je biki, amma Aku ya ƙi, ya ba su shawara su yi haƙuri da wanda Allah ya ba su. Suka bijire wa shawararsa suka fakaici idonsa su ka je wajen Mujiya suka roƙi ta ara masu gashinta za su je biki. Ita kuwa Mujiya ta ce,
“To! Duk wanda ya ba ni aron muryarsa zan yi masa gashi wanda ya fi nawa kyau.”
Ɗawisu ya kako muryarsa ya ba mujiya, ita kuwa sai ta yi ‘yan surkulle kafin ƙyaftawa da Bismillah sai gashin Ɗawisu ya canza duk ya koma ɗorowa da ja, fari da baƙi, makuba-mabuka, fari-fari, ɗorowa-dorowa da dai duk wata kala, Ɗawisu ya yi kyau.
Ganin haka sai duk tsuntsayen suka yi ta ribibin fiddo da muryarsu suna ba Mujiya tana yi masu gashi mai kyau.
Bayan ta gama karɓar muryoyinsu ta sanya cikin wata salka sai ta tambaye su ko akwai wanda ya ga makwarwa? Suka nuna ma ta inda makwarwa take ɓoyewa, Allah ya taimaketa, Makwarwa ta tafi ƙwarton gwaɗa, ta shiga cikin sheƙarta da ɗauki manyan ƙwaya-ƙwayi guda bakwai ta yi tafiyarta.
Aku bai san abin da ke faruwa ba, sai da marece, an zo dandalin rera waƙa duk wanda aka ce ya yi waƙa sai ya girgiza kai, ba baki sai kunne. Sarki ya yi baƙin ciki da abin da ya faru, ko da yake laifin su ne da suka tsallake maganarsa.
Tun daga wannan ranar duk inda tsuntsaye suka ga Mujiya sai su bi ta suna tsakuri har sai sun ji mata ciwo, ta ba su muryoyinsu da suka ba ta aro. Wannan ne ya sa Mujiya ba ta yawo da rana sai dare kada ta haɗu da tsuntsaye.
Daga wannan lokaci tsuntsaye suka bar yin magana sai aku kawai ke yi. Aku yakan tara mutanensa ya ba su labarin rayuwar duniya da yadda za su guje ta. A haka har Allah ya ɗaga aku ya kai shi ƙasar Hausa inda ya riƙi Sarauta. Duk faɗin ƙasar Hausa babu wanda bai san da zaman Waziri Aku ba.
Wasu Labarai
- Labarin Jatau Mawaƙi
- Labarin Akuya mai Magana
- Labarin Ƙaiƙayi Koma Kan Masheƙiya
- Labarin Na Shiga Ban Ɗauka Ba
- Labarin Sarkin Dawa
- Labarin Aikata Alheri Duk Inda Ka ke
- Labarin Ka So Naka, Duniya Taƙi Sa
- Labarin Ɓarawon Birni Da na Ƙauye
Ita kuwa Mujiya, da ta baro dabar tsuntsayen ta ci ribar abin da ta zo nema, ta sauko ƙasa kusa da garinsu ta yi birgima a ƙasa sai Mujiyar ta rikiɗe ta koma Jatau.
Ya yi ihu tare da kirari ya ɗauko salkar da ya aje muryoyin tsuntsaye ya haɗiye su baki ɗaya. Sannan ya kai wa uwarsa ƙwaya-ƙwayin makwarwa, ranar Bikin Shan Kabewa ta sa wa ɗanta Albarka.
Muryar Jatau ta yi daɗi, ya rinƙa rera waƙoƙi masu zaƙi da daɗin sauraro, sau da yawa ba don zaɓaɓɓun kalmomin da yake amfani da su ko fasaharsa wajen rera waƙa ake sauraronsa ba, sai don daɗin muryarsa. Jatau ya shahara sosai har Sarakuna ke kiransa yana rera masu waƙoƙi.
2 Comments
Allah ya kara maku basira, ina wa marubucin labarin fatan alkairi,
ReplyDeleteMasha Allah, Allah ya ƙara basira.
ReplyDelete