Talla

Labarin Akuya Mai Magana

 Zamanin Da Dabbobi Suke Magana

Daga: Littafin Hikimarka Jarinka na Bello Hamisu Ida

Can wani zamani da dabbobi suke magana. Kura, zaki ko damisa ba su cin sauran dabbobi, suna zaune lafiya tare da ba junansu shawarwarin zaman duniya, zaki shi ne sarkin dabbobi. Tsuntsaye da sauran dabobbi suna zuwa kasuwa su yi sayayya su dawo gidajensu, duk dabbobi suna magana, watau dai babu abin da Allah bai iya aikatawa. Sai dai Dabbobi ba su da cikakken wayau sosai, ba su da fasahar magana.

Akwai wata Akuya mai nacin magana da surutu ga gulma, duk abin da ta gani sai ta tanka, duk abin da ka yi gabanta sai ta je gaba ta ƙara. Wata rana uwar kiwonta cikin ta ya ɓaci, sai ta shiga kewaye tana gudawa. Ranar duk wanda ya shigo gidansu sai akuyar ta ce, “Inna yau ta daɗe a bayan-gida tana tutu, tun daga nan ina jin tusarta.”

Ranar sai da uwar riƙon ta ji kamar ta sayar da akuya. Mijinta na dawowa daga gona akuya ta lumshe ido tare da doɗe hanci da kofatonta, ta ce, “Baba wari kake yi, duk zufar noma da dauɗa a jikinka, ka je ka yi wanka.” Ranar ya ƙule sosai da wannan halayya ta akuyarsu, har suka yanke shawarar sayar da akuya. Washe gari suka kai ta kasuwa, amma duk wanda aka gaya wa cewa akuyar ta cika gulma da tsegumi sai ya fasa sayenta. Haka dai suka haƙura suka dawo da akuyar gida.

Wata marainiya da ake riƙo kusa da gidansu akuya, uwar riƙonta ba ta kyautata mata, kullum sai ta hana ta abinci, tun tana ƙarama, da ta yi wayau kullum sai ta fakaici ido ta shiga gidansu akuya da kwano ta buɗe tukunya ta saci abinci.

Wata rana uwar riko ta aike ta gidansu akuya, tana shiga sai ta iske babu kowa sai jaririn da aka bar wa akuya raino, ga sanwar abinci da aka aza, miyan marainiya ya tsinke ta buɗe tukunya ta ɗebi abinci cikin kwano ta ɓoye. Akuya ta shigo don rirriga jaririn da aka bar mata raino, taga Marainiya na satar abinci. Uwar Kiwo tana dawowa ta ga alamar an buɗe mata tukunya Akuya ta yi karab ta ce,

 “Marainiya ce ta buɗe maki tukunya ta ɗebi abinci, ina nan laɓe ina ganin duk abin da take yi.”

Uwar kiwon Akuya ta yi gajen haƙuri ta bi marainiya gidansu ta zazzaga wa uwar riƙonta bala’i.

Tana fita Uwar riƙo ta hau marainiya da duka har sai da ta karya mata ƙashin baya, ba’a daɗe ba Allah ya ɗauki ran marainiya.

Wasu Labarai

  1. Labarin Jatau Mawaƙi
  2. Labarin Akuya mai Magana
  3. Labarin Ƙaiƙayi Koma Kan Masheƙiya
  4. Labarin Na Shiga Ban Ɗauka Ba
  5. Labarin Sarkin Dawa
  6. Labarin Aikata Alheri Duk Inda Ka ke
  7. Labarin Ka So Naka, Duniya Taƙi Sa
  8. Labarin Ɓarawon Birni Da na Ƙauye

Labarin munafuncin da akuya ta yi wanda ya yi sanadiyar salwantar rai ya bazu cikin gari. Mai akuya ta fusata, hankalinta ya tashi, ta yi da na sanin abin da ta aikata, cikin fushi ta kama akuya, ta samu wasashiyar wuƙa ta yanke, sannan ta kai gangar jikinta cikin daji ta rataye bisa itace, ganin haka sai duk mutanen gari suka rinƙa kama dabbobi suna yankawa suna kaiwa daji su ratayewa bisa itace, duk sun gaji da gulma da dabbobi su ke yi.

Duk dabbar da ta ga gawar ‘yar uwarta sai ta yi cikin daji tana kuka da kururuwa. Dabbobi suka taru su ka yi shawara kowa ya cire muryarsa ya ba da, aka haƙa rami aka birne muryoyin, don su zauna lafiya a daina kashe su. Tun daga wannan ranar dabbobi ba su sake yin magana ba, amma duk abin da aka faɗa suna ji. 

 


Post a Comment

0 Comments