Talla

Khalifan Tijjani Sarki Muhammadu Sanusi Lamiɗo II Ya Ja Kunnen Mutane da cewa Kar su Bi Jam'iyya ko Addi a Zaɓɓukan 2023

#Arewanews

Daga: Muhammad Abdallah

09 Janairu, 2022

ABUJA, NAJERIYA - Khalifan Tijjaniyya na Najeriya Sarki Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga mutane waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a su je su yanki katin zaɓe kafin babban zaɓe na 2023.

Ya yi kiran ne a wajen taron shekara na tunawa da ranar haihuwar Fiyayyen Mazon Allah Annabi Muhammad (SAW).

Haka kuma, Sarki Muhammadu Sanusi ya yi kira ga mutane da cewa, idan zaɓen ya zo su zaɓi shugabanni na gari ba tare da la’akari da siyasa ko addini ba.

Ya ce,

Idan matasanmu suka samu aikin yi, tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya zai inganta. Mafi mahimmanci, mu ba jam’iyya ba ce, amma ba za mu iya naɗe hannayenmu mu yi watsi da siyasa ba.

Ya ƙara da cewa,

Duk dan Attijaniyya daga shekara 18 zuwa sama namiji ko mace, ku je ka karɓi katin zabe. Allah ya umurce ku da ku dogara ga hannun muminai amintattu.

Ya kuma ce,

Yanzu muna wani lokaci da jama’a ne ke da ikon naɗa shugabanni, ƙuri’arku ita ce ƙarfin ku, kuna da nauyi a kanku.

 Wasu Rahotanni

  1. Rundunar Sojojin Najeriya ta Gargaɗi Sheikh Ahmed Gumi
  2. Osinbajo Ya Tafi Ghana Don Wakiltar Shugaba Buhari A Taron Ecowas
  3. Buhari Ya Nemi Mutanen Zamfara Su Ƙara Haƙuri

Sarkin Muhammad Sanusi II ya halarci taron ne inda ya gabatar da jawabinsa. Sarkin mutum ne mai fari jini da son mutane da kiraye-kiraye ga al'umma.

Post a Comment

0 Comments