Talla

Ka So Naka, Duniya Ta Ƙi Sa

Labarin Alhaji da kishiyar Uwarsa

Daga: Littafin Hikimarka Jarinka na Bello Hamisu Ida

Alhaji sunan wani yaro ne da uwarsa ta rasu tun yana ɗan jariri, mahaifinsa kuwa ba mazauni ba ne, don haka sai ya damƙa amanar riƙonsa hannun kishiyar uwarsa Laraba, tana da ɗa guda ɗaya wanda ta ɗauki son duniya ta aza masa.

Laraba irin matan nan ne marasa imani, ga son zuciya da ƙaunar abin duniya. Kullum gurinta ta muzguna wa Alhaji, ta daɗaɗa wa ɗanta mai suna Yakubu.

Duk wata hanyar shegantaka da lalacewa can take tura Alhaji. Gurinta ya lalace ya zama mutumin banza, ɓarawo mai shaye-shaye da satar kayan mutane, Amma cikin hukuncin rabbana, Allah ya kare sa daga waɗannana munanan halaye.

Duk lokacin da ta tura sa dabar ɓarayi sai Alhaji ya kama hanya ya nufi wata makaranta ya zauna bakin ƙofar makarantar yana sauraron karantun da ake wa ɗaliban makarantar, Allah ya yi shi da son karatu bai samu dama ba.

Wata rana wani malami ya fito yaga Alhaji, ya kama sa ya sa shi a wannan makarantar. Duk abin nan da ke faruwa Laraba ba ta da masaniya, ta ɗauka kullum Alhaji in ya fita wajen ɗaukar magana yake zuwa, ashe abin ba haka yake ba, Alhaji yana makaranta. Shi kuwa Yakubu kullum yana kusa da ita, yana fitina kala-kala. Daga ya ce ta sai masa alewa sai ya ce ta sai masa soyayyen kifi da dai kayayyakin ƙwalama.

Rannan Laraba ta yi mafarkin Alhaji ya zama babban Malami, ga kuɗi ga ilimi mutane sun taru ƙofar gidansa sai karɓar sadaka suke yi, cikin masu karɓar sadakar har da ita. Firgigi ta tashi, ta tsorata da wannan mafarki, ko kaɗan ba ta ƙaunar Alhaji balle ta ƙaunaci ci gaban rayuwarsa. Ko Sallar Asuba ba ta yi ba, ta nufi gidan boka ta zayyana masa mafarkinta.

Boka ya ce da ita,

“Kar ki damu don wannan mafarkin, zan ba ki wani garin magani ki zuba masa a tuwon dare, yana ci zai bugu,  da tsakar dare ki tashi ki ɗauke shi bisa makara ki fita ta ƙofar Mata har zuwa bayan gari, akwai wani ramin macizai, ki jefa sa ciki, daga nan kin huta babu wanda zai ƙara jin duriyarsa.”

Laraba ta yi murna da wannan magani na boka, ta ba shi abin karya kumallo ta tafi gida, tana shiga gida ta sami Alhaji a shigifa yana ta rera waƙa, wace ta jeranta ƙofofin Kano yana cewa,

Kai ka isa ɗan Kano?

Eh, na isa ɗan Kano.

In ka isa ɗan Kano,

Ƙofa nawa ka sani?

Ƙofar Mazugal na sani,

Jakara ma na sani,

Ƙofar Wambai na sani,

Ta Mata ma na sani,

Nasarawa ma na sani,

Kansakali na sani,

Da Kabuga na sani,

Kofar Ruwa na sani,

Da Na’isa na sani,

Duk dai cikin Kano.

Tana shigowa Alhaji ya durƙusa har ƙasa ya gaishe ta. Duk cutawar da take masa bai fasa yi mata biyayya ba, ta ƙara harzuƙa ta sanya ƙafa ta hamɓarar da shi can gefe.

Da dare Laraba ta aikata yadda boka ya umurce ta, ta ɗauki Alhaji saman mankara ta kai sa wannan rami ta fiddo sa ta jefa sa cikin ramin macizai.

Wasu Labarai

  1. Labarin Jatau Mawaƙi
  2. Labarin Akuya mai Magana
  3. Labarin Ƙaiƙayi Koma Kan Masheƙiya
  4. Labarin Na Shiga Ban Ɗauka Ba
  5. Labarin Sarkin Dawa
  6. Labarin Aikata Alheri Duk Inda Ka ke
  7. Labarin Ka So Naka, Duniya Taƙi Sa
  8. Labarin Ɓarawon Birni Da na Ƙauye

Ta dawo gida tana murna, tun daga wannan rana farin ciki ya mamaye rayuwarta, ta rabu da ƙwallon mangoro ta huta. Ta ƙara ɗaukar wani tsananin so ta ɗora wa Yakubu, saboda yanzu shi kaɗai ne gaban mahaifinsa. Ta koma wajen boka ana rufe bakin mijinta kada ya tambayi labarin Alhaji.

Ashe duk macizan da ke ciki ba macizai ba ne, hadimai ne na wani mashahurin Malami mai zuhudu a zuciya, a ƙalla shekarunsa hamsin a cikin wannan kogo babu abin da  yake yi sai ibada  da bautar Allah maɗaukakin sarki.

Waɗannan macizai aljannu ne daga cikin hadimansa da suke masa hidima. Mafi yawan Bokayen wannan zamani irinsu Boka Kutumbi, Boka Kumbaru, Boka Na-yaji, duk sun ɗauka wasu azababbun macizai ne, shi ya sa suke halakar da mutane ta hanyar jefa su cikin wannan rami.

Alhaji na faɗawa cikin ramin ya kirayi sunan Allah, macizan suka rikiɗe suka zama mutane sannan suka sungumi Alhaji sai gaban Shehi Ɗalibu Bn Mas’ud. Ya yi mamaki sosai da ya ga Alhaji yaron da bai wuce shekara bakwai ba ga ladabi, a hankali Shehi ya shiga bincikar rayuwar Alhaji, ya ga komai ƙarara tun daga ranar haihuwarsa har zuwa lokacin da Laraba da jefo shi wannan rami da nufin ya mutu.

Shehi ya tausaya masa sosai, nan ya shiga koyar da shi darusan ilimomi. Wannan rami yana ƙumshe da alatu irin su darduma, kilisai, Alkabbu, da kuma dukiya irin su zinarai, azurfa da tagulla, sannan kuma akwai itatuwa irin su inibi, ayaba, tuffa, gwanda, dabino, da abarba sannan kuma akwai abinci da aljannun suke kawowa daga ƙasa mai tsarki wato Madina.

Kafin ka ce kwabo Alhaji ya canza, jikinsa ya yi kyau sosai, uwa-uba ya haddace Ƙur’ani mai girma. Da Shehi ya ga Alhaji ya zama mutum aƙalla yanzu ya kai shekara goma sha takwas, sai ya ce ya koma garinsu ya rinƙa koyar da mutane sanin Allah.

Shehi ya ɗauki dukiya mai tarin yawa ya ba Alhaji sannan ya yi masa alƙawarin zai rinƙa kawo masa ziyara duk ranar Juma’a da dare, ya ƙara yi masa alƙawarin ba zai taɓa yin talauci a duniya ba, duk lokacin da yake da buƙatar dukiya ya zo ya ɗibi irin wacce yake so.

Suna kuka suka rabu da juna. Alhaji ya dawo cikin birnin Kano. Kafin ka ce me, labarin shaharar Alhaji ta karaɗe ƙasar Hausa, watau Garuruwan Hausa bakwai da garuruwan Banza bakwai. Nan fa mutane suka rinƙa kwararowa zuwa wajen Alhaji neman ilimi, duk bayan La’asar Alhaji zai fito ƙofar gidansa ya tara mabuƙata ya yi ta masu sadaka.

Wata rana yana cikin ba da sadaka sai ya ga Laraba cikin layi ita ma za ta karɓi sadaka. Alhaji ya je har inda take ya kama ta ya ɗaga ya ce, “Uwar riƙota sannun ki.”

 Ya ɗuka har ƙasa ya gaishe ta, Laraba ta saki baki tana mamaki, ba ta san ko wane ne wannan bawan Allah ba, ta samu labarinsa, ita ma ta zo neman taimakonsa.

Alhaji ya ja ta cikin gida sannan ya gaya mata ai shi ne Alhaji. Laraba ta faɗi somammiya, bayan ta farfaɗo Alhaji ya sanya haɗimansa suka yi mata sutura suka ba ta abinci mai daɗi ta ci. Duk lokacin da ya fito sai Laraba ta duƙa tana afi da neman afuwarsa.

Shi kuwa ya tambaye ta inda mahaifinsa yake da ɗan’uwansa, Laraba ta fashe da kuka ta ce, “Ɗan’uwanka ya samu taɓin hankali sakamakon barasa da ya rinƙa sha, mahaifinka kuwa, baƙin cikin halin ɗan’uwanka da rashinka da ya yi ya kashe shi.”

Alhaji ya yi salati ya sanar da Ubangijin rahma, haka Allah ya hukunta masa rayuwa, bai ce komai ba sai Addu’o’i da yake yi. Tun daga wannan rana ya riƙi Laraba a matsayin uwa, sai dai yana taka-tsan-tsan da rayuwarta, duk da yake ta saduda sosai, duniya ta koyar da ita darasi.

Kullum in ya yi Sallah sai ya yi sadaka ya roƙi Allah ya albarkaci kabarin mahaifansa, ya warkar da Ɗan’uwansa, ya shiryar da Laraba tare da duk wata mace mai irin halinta.

Bayan ya cika shekara sha tara ya samu ɗiyar limamin garinsu ya aura, Aisha sunanta yarinya mai hankali da sanin darajar mutane ga ilimin muhammadiya. Allah ya albarkace su da zuriya. Duk lokacin da ya bushi iska yakan je wajen Shehi su yi karatu tare da zumunci.

 


Post a Comment

0 Comments