Talla

Jiragen Yaƙi Na Super Tucano Sun Kashe Kwamandan Iswap

 Daga: Muhammad Abdallah



ABUJA, NAJERIYA - sojojin sama na Najeriya sun gudanar da wasu sabbin hare-hare da yawa a maɓoyar da mayaƙan ƙungiyar ISWAP ke zaune. Kisan ya biyo bayan harin da jeragen na super tucano suka kai, jiragen dai na daga cikin jiragen da ƙasar ta siya don yaƙar tsageru masu tayar da ƙayar baya a cikin ƙasa.

Jiragen ƙirar super tucano sun kashe shugaban ƙungiyar ISWAP a Kirta Wulgo dake Jiar Borno a wannan sati. Jaridar PR Nigeria ce da ruwaito cewa, hare-haren sun yi sanadin mutuwar babban Kwamandan kungiyar mai suna Mallam Ari da ke kula da yankin na Kirta Wulgo.

Sanarwar ta ƙara da cewa,

"Wani babban jami'in rundunar sojan Najeriya ya ce hare-haren ta sama, waɗanda aka kaddamar bayan an samu bayanan sirri, sun tabbatar da mutuwar fiye da 'yan ta'adda guda arba’in waɗanda suke taruwa a gefen Arewa maso gabashin Kirta Wulgo, kusa da inda aka dasa tutar waɗanda ake zargin 'yan ƙungiyar ISWAP ne,"

Jiragen yakin sun kashe wasu sojojin-haya da ke ƙera wa mayakan ISWAP bama-bamai. Kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, wanda ya tabbatar da kai hare-haren ta sama a yankin na Kirta Wulgo, bai ce komai ba game da yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Garuruwan Katsina da Zamfara da Kaduna da Sokoto da Kebbi da Nija da Borno da ɗaya daga cikin garuruwan dake fama da tashe-tashen hankulla da ɓarayi masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa da kuma ɓarayin ISWAP da yan Boko Haram. Kodayake jami’an tsaro da gwamnatin ƙasar na iyakacin ƙoƙarinsu wajen fatattakar tsageru daga cikin ƙasar.

Wasu Labarai:

  1. Wani Matashi Ya Rataye Kansa A Jigawa
  2. Wasu Matasa Sun Ƙona Makarantarsu Hanifa Yarinyar da Wani Malaminta Ya Kashe A Kano
  3. Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Ɓarayin Daji A Yankunan Zamfara

Post a Comment

0 Comments