Hauwa’u Bello
ABUJA, Najeriya - Jarumar
kudancin Najeriya a firar ta da yi a ranar 13 Janairu 2022 wadda aka fi sani da
Caroline (Hutchings) Danjuma, ta bayyana yadda ta ji bayan rabuwar aurenta,
ta faɗi irin halin ƙunci da ta shiga bayan rabuwar ta da tsohon mijinta mai
suna Musa Danjuma.
Jarumar a shafinta na Instagram
ta ce, ta zargi kanta da rashin yin kyakkyawan zamantakewar aure ta kuma gane
irin kuskuren da ta tafka bayan ta bar gidan aurenta, wanda sai daga bisani ta fahimci
ba ƙaramin sakaci bane barin gidan miji.
A cewarta, ta sha fama da munanan
kalamai da izgili daga abokai da kuma wasu mutane waɗanda ba su san ainihin
abin da ya faru ba wanda ya yi sanadiyar rabuwar aurenta.
A shafinta ta rubuta cewa,
“Na zargi kaina da rashin yin
kyakyawan zamantakewar aure, na ɗora wa kaina laifin duk da cewa lokacin auren
na ɗauka bani da lafiya, amma sai bayan na rabu da gidan miji na fahimci cewa
ba wata rashin lafiyar da ta same ni”
Ta ƙara da cewa,
"Na yi addu'a ga Allah don
ya yi mani taimako mafi mahimmanci sannan ya gafarta mani bisa zunuban da na
aikata”
Rabuwar aure ga taurarin fim ba
wani baƙon abu bane, ko baya-bayan nan Mansura Isa fitacciyar jarumar Kannywood
wadda ta auri Sani Danja har suka samu haihuwa tare, ta bayyana yadda aurenta
ya salwanta, ta kuma bayyana irin ƙuncin da ta shiga bayan rabuwarta da mijinta
duk da yake kuwa ta ce har yanzu akwai kyakyawar alaƙa tsakaninta da tsohon
mijinta. An sha ganinta a shafukan shada zumunta musamman TikTok tana bayyana
halin zawarci da take ciki.
Wasu Labarai:
0 Comments