Daga: Muhammad Abdallah
ZAMFARA,
NAJERIYA — Wasu mahara wanda ake tsammanin ɓarayin
daji ne sun shiga wata unguwa da ake kira da Mareri dake birnin Gusau da
daddare don su sace wani mutum, amma rundunar ‘yansandan Jihar sun yi ƙoƙari
sosai wajen murƙushe wannan hari, inda suka yi bata-kashi tsakanin ‘yansandan
da ɓarayin dajin, daga bisani ɓarayin suka ruga suka shiga daji. Bayan haka
kuma sai jami’an suka yi masu kwantar bauna sannan suka samu damar amsar wasu
da ɓarayin suka yi garkuwa da su kafin su shiga unguwar Mareri.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara SP
Muhammad Shehu ya shaida cewa an sanar masu da zuwan ɓarayin, sai suka aika da
jami'ansu inda suka hana ɓarayin dajin tafiya da mutanen da suka sata.
Haka kuma, a yankin Bukuyum jami’an tsaro sun
fatattaki wasu ɓarayin daji har suka samu damar kashe wasu ɓarayi da dama
sannan suka kori wasu suka kuma kuɓutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su.
Wani ganau ya shaida cewa, an yi musayar wuta sosai tsakanin ɓarayin dajin da
jami’an tsaro wanda daga baya Allah ya ba jami’an tsaro nasarar fatattakar ɓarayin
dajin. An yi wannan arangama ne a dajin Gando.
Wani ganau ya shaida cewa, ɓarayin sun koro
mutane daga ƙauyukansu inda suka riƙa satar abinci da shanaye, amma daga baya
sai jami’an tsaro suka zo sannan suka kori ɓarayin. An kashe wasu ɓarayin daji
da dama a wannan fafatawa. Saidai babu wanda ya ji ciwo a ɓangaren jami’an
tsaro.
Ɓarayin daji dai na ƙara kai hare-hare a ciki
da wajen jihar Zamfara, duk da kiraye-kirayen da wasu shuwagabannin ɓarayin
suke yi na neman sasanci, ko a watannin da suka wuce saida Bello Turji ya saki
mutanen da ya kama a ƙoƙarinsa na yin sasanci da gwamnati.
Kdoayake, jami’an tsaro na taka muhimmiyar
rawa wajen daƙile duk wani hari da ɓarayin dajin za su kai ko suka kai. Ko baya,
bayan nan saida Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da rundunar hari ta
fatattakar ɓarayin daji a wani yunƙuri na samar da zaman lafiya a jihar Neja,
inda ke samun hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin
fansa.
0 Comments