Daga: Muhammad Abdallah
12 Janairu,
2022
ABUJA,
NIJERIYA - Shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari ya janye haramcin da ya saka wa Kamfanin Twitter a ƙasar.
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya tabbatar da janye
haramcin yin amfani da manhajar dandalin Twitter a cikin ƙaasar. Bayan janye haramcin, ana
tunanin cewa daga ranar 13 ga watan Janairu shekara ta 2022 tokar janyewar zata
fara aiki, inda ɗinbin yan Najeriya za su ci gaba da aiki da dandalin na sada
zumunta.
Najeriya ta kakkaɓa wa kamfanin haramcin
gudanar da ayyukansa da faɗin ƙasar ne a watan Yuni ta shekarar 2021, gwamnati
dai ta yi zargin cewa matasa na amfani da shafin wajen yaɗa abubuwan dake
haddasa tashe-tashen hankulla a cikin ƙasa. An taɓa yi amfani da shafin ne
wajen asassa wutar Endsass wato kiraye-kirayen da wasu matasan ƙasar suka riƙa
yi don a dakatar da Yansandan da aka fi sani da SASS.
Duk da zama da kiraye-kirayen da
hukumomi suke yi, ƙasar ta yi tsayin daga a kan cewa ba zata buɗe kamfanin ba
har sai ya cika wasu sharuɗɗa ciki harda biyan ƙasar haraji. Ko a shekarar data
gabata dai kamfanin Twitter ya buɗe babban ofishinsa a makwabciyar ƙasar.
Ko ɗage haramcin zai sake buɗe
wani sabon shafi a cikin ƙasar Najeriya, ko kuwa yan ƙasar za su rungumi wani
dandalin sada zumunta kamar yadda suka rungumi Fesbuk da Tiktok da Instagram da
sauran dandali na sada zumunta?
Wasu Labarai:
0 Comments