Talla

Gwamnatin Najeriya Ta Ƙaddamar Da Harin Fatattakar Ɓarayin Daji

 Daga: Aminu Abdullahi Muhammad

ABUJA, NAJERIYA — Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da rundunar hari ta fatattakar ɓarayin daji a wani yunƙuri na samar da zaman lafiya a jihar Neja, inda ke samun hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa. A hannu ɗaya kuma maharan Boko Haram suna ƙara samun mafaka a dazuka bayan sun gudo daga yankunan Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas na cikin ƙasar Najeriya.

Mallam Garba Shehu ya ce, a wani umarni da Shugaban ƙasa ya bai wa Hedikwatar tsaro kwanaki ƙalilan da suka wuce, Muhammadu Buhari ya buƙaci sojoji su mai da martani mai ƙarfi don kawo ƙarshen hare-haren ɓarayin daji a yankunan Neja.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya yi jaje ga waɗanda hare-haren ɓarayin dajin ya rutsa da sun a makwannin da suka wuce.

Mallam Garba Shehu ya ce, manufar ƙaddamar da rundunar fatattakan ɓarayin daji shi ne don magance matsalolin tsaro da kuma korar ɓarayin daji masu addabar mutanen yankin.

Malam Garba ya ƙara cewa,

''Bayanai sun nuna cewa 'yan fashin daji da ake fatattaka daga jihohin Zamfara sun fara kwarara jihar Neja, gwamnatin jihar ta tabbatar har 'yan Boko Haram sun ƙetaro tare da fakewa a dazukan da ke Neja”.

Ya ci gaba da cewa,

“Wannan matsala tana damun shugaban ƙasa, don haka ya bada umarni aje dazukan a kuma fatattaki waɗannan mutane. Kuma da yardar Allah za a ga abin da zai biyo bayan wannan aiki.''

Garba Shehu ya ce, tuni aka fara wannan aiki, nan take shugaban ƙasa ya bada umarnin a fara aiki kuma mayaƙa da jiragen sama sun fara aiki. Ya kuma yi bayanin cewa, rashin netwok ne ke sanyawa ba a samun cikakkun bayanai na ci gaba da ake samu, amma nan gaba kaɗan Hedikwatar tsaro ta Najeriya za ta fitar da cikakkun bayanai a kan ci gaban da ake samu ta ɓangaren kawo tsaro a cikin ƙasa.

Jihar Neja na ɗaya daga cikin jahohin dake fama da matsalolin tsaro, tun daga ɓarayin daji da Boko haram waɗanda gwamnati ta ce an samu ƙaruwarsu sosai a waɗannan watanni. Duk dayake, gwamanti na iyakacin ƙoƙarinta wajen kawo ƙarshen tashe-tashen hankulla.

Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Neja da Kebbi an fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don samun kuɗin fansa.

Wasu Labarai:

  1. An Kama Wanda Ya yiwa Tsohuwa Fyaɗe
  2. Dattawan Arewa Sun Ce Shugaba Buhari Ya Basu Kunya
  3. Yadda Yan Wasan Najeriya Suka Lallasa Masar da Sudan

Post a Comment

0 Comments