Talla

Gobara ta laƙume kasuwar Nguru a Jihar Yobe

 Daga: Hauwa'u Bello

8 Janairu, 2022

ABUJA, NIJERIYA - Gobara ta tashi a babbar kasuwar Nguru dake babbar birnin Yobe. Gobarar ta fara cin shaguna da misalin ƙarfe takwas na safiyar yau asabar.

Waɗanda abun ya faru a gabansu, sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga sashen ƴan takalma da kuma ƴan robobi kuma ta laƙume shaguna masu yawa waɗanda ake saide-saide a cikinsu.

Tuni dai jami'an kai agaji da kuma na kashe gobara suka isa wajen domin kashe gobarar.

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen Jihar Yobe wato ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce,

Tuni jami'an kashe gobara da matasa suka haɗa hannu inda suke ƙoƙarin kashe gobarar.

Haka kuma ya tabbatar da cewa ƴansanda da sauran jami'an tsaro sun isa wurin domin tabbatar da tsaro a ciki da wajen kasuwar.

Goraba dai tasha yin illa ga kasuwannin dake Arewacin Nijeriya, ko a watannin da suka gabata gobara ta kama babbar kasuwar Katsina da Sokoto.

Post a Comment

0 Comments