(An bi Mazhabar Farfesa Ibrahim Malumfashi wajen rubuta labarin)
Rubuta Labari: Bello Hamisu Ida
Ana Kasuwanci da dillancin Labarin a kafar sadarwa ta Facebook da WhatsApp da YouTube, za a iya samun copy na littafin a daftarin PDF a shafin www.arewanews.org.ng ko a samun sautin Audio na Littafin a manhayar YouTube a tashar Kannywood TikTok.
****
FARKON LABARI
Jihar Katsina, Ƙaramar Hukumar Jibia, Ƙauyen Kufan Daga
Ranar 10 Janairu, 2018
A hankali wasu baƙaƙe hawaye suka fito daga idonsa, ba hawayen baƙin ciki ba ne, bana farin ciki ba, ba na takaici ba, ba kuma na nadama ko danasanin abinda ya aikata ba. Baya daga cikin ɓarayi daji ko infoma ko gurɓatattun jami’ai ko ɗaya daga cikin masu yiwa ɓarayi safara abinci ko makamai ko man fetur ko safarar ‘yan mata. Shi malamin makaranta ne, kuma Hedimasta wanda ya ke alfahari da malamtakarsa.
Wajen da suke zaune babu taga, ba gado, ba katifa ko mashimfiɗi, ba kewaye ba silin ba kujeru balle masanyar iska, ɗaki ne kamar dai kwai, bambancinsa da kwai dogon ɗaki ne mai ƙofa ɗaya. Akwai a kalla mutane hamsin zuwa hamsin da tara. Dukkan mutanen da ke cikin ɗakin fursunoni ne dake jiran hukunci, wato waɗanda suke shari’a.
Wani dattijo ya matso kusa da Abdallah, dattijon yana daga cikin tsofin fursunoni da aka kasa ƙarasa shari’arsu, a kalla ya fi shekaru goma zuwa sha biyar a gidan kason, ko a lokacin da aka kawo shi gidan kason zai haura shekara arba’in da biyar. An kawo shi ne bisa zargin yiwa wata yarinya fyaɗe da kuma kasheta. Kodayake ba shi ne asalin wanda ya yiwa yarinyar fyaɗe ba amma dai an ga gawar yarinyar a hannunsa.
Dattijon wanda ake cewa Sarkin ɗaki ya ce,
“Abdallah ka daina saka damuwa a zuciyarka”
Ya kale shi, cikin takaici ya ce,
“Sarki dole in saka damuwa a raina, an raba ni da iyalina bisa laifin da ban aikata ba”
Sarkin ɗaki ya ce,
“Ni kaina da ka ke gani ana tuhuta ne bisa aikin da ban aikata ba”
Abdallah ya kale shi, wani hazo-hazo da duhu suka dabaibaye zuciyarsa, a hankali ganinsa ya fara ɗaukewa, akwai wasu hotuna da suke gilmawa a cikin kwalwarsa, akwai hoton wasu mutane da suka fi wucewa, hoton Maigari da Sarkin Kasuwa da Sarkin Fawa da kuma Ɗantamaro, shi ɗantamaro jikan Maigari ne kuma ƙasurgumin ɓarawo da ya sani a makarantar da yake koyarwa inda yake riƙe da shugaban makarantar wato Hedimasta. Yanzu da yake ganin hotunansu a cikin kwalwarsa zuciyarsa na raɗaɗi ya tuna ranar farko da ya fara haɗuwa da su.
A ranar litinin ce, wace ake wa kirari da Litinin ranar aiki ko nasara na tsoron ki. A ranar da misalin ƙarfe shidda da rabi na safe, Abdallah ya kamala shiryawa ya ɗauki litattafansa da rigar sanyi, ya fita, daidai ya isa bakin ƙofar gida ne matarsa ta biyo shi da sauri, akwai alamar barci a fuskarta, akwai kwantsa akwai miyan barci haka kuma gashin kanta duk ya yamutse.
Ta hangame bakinta tana hamma, bayan ta ɗan rufe bakinta da hannu ta ce,
“Haba Malam Audu, ka tsaya ka yi kalaci mana sannan ka tafi makarantar”
Ya kale ta ya ce,
“Ke da yanzu ki ka tashi daga barci, yaushe har ki ka haɗa kalacin da zan ci”
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce,
“Tun ranar Juma’a nake faɗa maki cewa an yi mani transfa zuwa wata makaranta dake ƙauyen Kufan Daga, kuma can ma ni zan riƙe Hedimasta, an ce ƙauyen yana da nisa, dole sai na tafi da wuri”
Ya kale ta sosai sannan ya ce,
“Na aje kuɗin cefane gefen katifa ta”
Daga haka bai sake cewa komai ba, ya tura mashin ɗinsa ƙirar Jenchain ƙarfe, ya fita. Duk da yake mashin ɗin ya kwana biyu, amma bugu ɗaya ya yi masa ya tashi.
Akwai hazo da buji da iska, akwai muku-mukun sanyi. Kodayake Abdallah ya sanya rigar sanyinsa, amma sanyi ya kan ratsa fatar jikinsa ya shiga cikin ƙasusuwansa. Haka ya daure ya ci gaba da tafiya har ya fita gari sannan ya raɓa ta gefen babbar Hedikwatar ‘yansanda dake garin, ya bi bayan gidajensu ya ratsa ta wani birji ya ci gaba da tafiya, yana wuce gonaki da ruga da ƙananan ƙauyuka. Sai da ya yi tafiyar kilomita arba’in da biyar.
Wani lokacin ya kan yi kiliya da masu ɗaukar itace ko mutane bisa jakuna sun nufi wajen ɗibar ruwa, ko ‘yan gwarama masu ɗaukar shinkafa bisa tsofin motoci wasu kuma saman mashina sun ɗauko buhun shinkafa uku da man olga. A haka ya samu ya isa babban ƙauyen Kufan Daga.
Lokacin da ya isa tsakiyar garin, akwai mutane a wata ‘yar yara suna ta saye-saye da yin kalaci a wajen wasu yara, wasu yaran ƙanana ne wasu matsakaita wasu kuma ‘yan mata, ga alama babu abinda ba a saidawa a cikin ‘yar yarar.
Cikin Abdallah ya ɗan motsa, sai yanzu ya tuna cewa bai yi kalaci ba, ya matsa kusa da ‘yar yara. Dukkan mutanen da ke wajen suka maido hankalinsu wajensa. Ya nazarci abincin da ake saidawa, ya matsa kusa da wata yarinya wacce abincinta ya fi sauran tsafta.
Ya ce,
“Nawa abincinki?”
Ta yi masa kallon rashin sani, ta ce,
“Naira ɗari duk kwano ɗaya”
Ya ce mata,
“Za ki bani har da kwanon, sai in maido maki anjima idan an tashi daga makaranta?”
Ta ɗanyi rau-rau da itanuwa, ga alama yarinyar ta fara lissafin gandi, ta ce,
“Babu komai”
Ya ɗauko kuɗi ya bata, yarinyar ta karɓa cikin girmamawa ta adana kuɗin cikin wata ‘yar jaka, ta bashi kwanon abinci ɗaya. Bayan ya ƙarɓi kwanon ya ce,
“Don Allah ina ne makarantar Firamare ta wannan gari?”
Ta sake kallonsa cikin girmamawa ta ce,
“Ko kai ne sabon Malamin da za a kawo mana?”
Sai yanzu ya ƙara fahimtar dalilin da yasa yarinyar take da natsuwa sosai, ga alama ɗaliba ce a makarantar da aka maido shi yanzu.
Ya ce mata,
“Eh, ni ne. Kema can makarantar ki ke”
Ta ce cikin girmamawa,
“Eh, malam ai ni ce shugabar ɗalibai mata wato head-girl ta makarantar”
Ta yi shiru, ta ɗan yi dube-dube, sannan ta kira wani yaro, suna kama sosai da yaro, ƙila shi ne ƙaramin ƙaninta. Ta ce da yaron,
“Ga sabon Malami an kawo, ka raka shi ƙofar gidan Maigari”
Ta maido hankalinta wajen Malam ta ce,
“Malam bari ya raka ka gidan maigari, daga a bayan gidansa ne makarantar take”
Abdallah ya yi godiya, kodayake ɗalibarsa ce, amma tana da hankali sosai. Daidai lokacin da zai juya ya tafi ya ji yarinyar na shelatawa ga sauran yaran dake kusa da ita tana ce masu,
“Ku yi sauri ku kamala kasuwarku mu tafi makaranta, an kawo sabon Malami”
Suka isa ƙofar gidan Maigari, yaron ya shiga ya yi sallama da shi. Cikin girmamawa Maigari ya fito, suka gaisa sannan ya raka shi har cikin makaranta suna tafiya suna taɓa fira. Maigari da kansa ya ɗauko mukulai ya buɗe ofishin Hedimasta. Suka shiga, Abdallah ya zauna bisa sabuwar kujerarsa.
Maigari ya yi gyaran murya ya ce,
“Malam sai an yi haƙuri, yaran suna zuwa wajen ƙarfe goma idan sun kamala komai na gida”
Duk da yake Abdallah ya ji wani iri a cikin ransa amma sai ya wayance ya ce,
“Babu komai Ranka shi daɗe, zan jira su har su iso”
Ya ɗan yi shiru ya ce,
“Ranka shi daɗe ai kaga sauran malaman ma basu iso ba, dama mu uku ne za mu ci gaba da koyarwa”
Maigari ya ce,
“Eh, waɗancan ma da suka tafi su uku ne”
Bayan sun ɗan taɓa fira Maigari ya yi bankwana ya tafi. Abdallah ya gyara wajen zamansa sannan ya kakkaɓe litattafan dake cikin ofis ɗin. Dogon ofis ne, akwai kujeru akwai teburin hedimasta da kujerun zama da allon ɗalibai da allon malamai da kuma allon shuwagabannin da suka taɓa riƙe hedimasta a makarantar. Akwai litattafai masu tarin yawa, ga alama ɗakin karatun makarantar na cikin ofishin hedimasta.
Abdallah ya ɗauki alƙalami ya je ya rubuta sunansa a saman allon waɗanda suka taɓa riƙe hedimasta a makarantar. ABDALLAH MUHAMMAD BELLO ya rubuta.
Yana nan zaune Head-girl ta shigo, sanye da kayan makaranta da jikar makaranta da kuma tabarmar zama. Bayan ta shiga ajinsu ta aje sannan ta dawo ta gaida Malam Abdallah, ta ce,
“Malam za mu yi sharar ofis”
Abdallah ya ce,
“To shi kenan, ya sunanki ne”
Ta yi murmushi fararen haƙoranta suka fito, fara ce doguwa bafillatana, amma tana da sirki da wata ƙabilar bayan Fulani. Ta sadar da kanta ƙasa ta ce,
“Sunana Lubabatu”
Daga haka basu sake yin magana ba, ya fito waje, ya zauna, ta ci gaba da shara. Ɗalibai suka fara zuwa da ɗai-ɗaya, wasu na taya Lauratu shara wasu kuma na shigewa ajinsu. Amma duk wanda ya zo sai ya gaida sabon Malaminsu.
Ɗalibai sun taru, sauran malamai sun zo makaranta, an share makaranta saura fara karatu. Kowa ya hallara gaban ofis ɗin hedimasta don yi asambili. Ana cikin yin addu’a sai suka ji ƙarar mashina, kowa ya saurara, suna kallon waɗanda za su zo a saman mashinan.
Kodayake, ɗaliban makarantar sun san ko su waye, sun kuma san abinda suka zo yi. Wasu mashina kirar Boksa suka shigo harabar makarantar, a kalla mashinan za su kai guda goma, kowanensu na ɗauke da mutum ɗaya. Dukkan mutanen dake saman mashinan sun yi rawani wanda ya rufe fuskokinsu. Amma mutum ɗaya daga cikinsu bai rufe fuskarshi ba, kuma shi kaɗai ne saman mashin ɗinsa.
Ba su rike da ko tsinke balle ayi tunanin satar mutane ko korar shanu ko kassara wani suka zo yi ba.
Matashin dake gaba, ya sauko saman mashin ɗinsa, cikin isa, ya samu waje ya tsaya, yana kallon daidai inda Abdallah ya ke tsaye. Ya kalli Abdallah, Abdallah ya kale shi. Wani daga cikin yaransa ya matso kusa da shi, ya ce,
“Wannan shi ne sabon malamin da aka kawo”
Malamin da yake addu’ar ya tsayar da addu’arsa sannan ya ce kowa ya shiga aji, ya matsa kusa da Abdallah ya ce,
“Malam Audu wannan shi ne Ɗantamaro, jikan Maigari ne”
Abdallah da Ɗantamaro suka yi kallon-kallo.
***
Wasu Labaran Hikaya
1 Comments
Da kyau Allah ya kara vasira
ReplyDelete