Daga: Bello Hamisu
05 Janairu, 2022
KANO, NIJERIYA — Fim ɗin ‘Makaranta’ Fim ne da Arewa Age Moɓie Production dake
nuna fina-finanta a yanar gizo ta nuna tallar shi, Aminu Umar Mukhar ya yi Diraktin
na Fim ɗin. Fim ɗin ya ja hankali ne saboda yadda aka koyar da Ilimin Jima’i a
cikinsa. Kodayake har yanzu ba a saki cikakken Fim ɗin ba, amma dai daga kallon
tallar da yadda taurarin cikin Fim ɗin suke taka rawa tare da faɗin kalmomin
batsa za a fahimci cewa Fim ɗin yana koyar da ilimin Jima’i da yadda mata za su
riƙa kare kansu daga yawan yin Jima’i.
Kodayake wasu na ganin cewa Fim ɗin
zai taimaka sosai wajen ɓata tarbiya musamman yadda aka ji wasu taurarin Fim ɗin
na ambaton kalmomi da jimloli na batsa.
Misali an ji wata tauraruwa na ce,
“Jima’i, Jima’i, me ke faruwa bayan tarayya?”
Haka kuma an ji wata malama na cewa, “The external opening of virginal…”
Duk a cikin Fim ɗin an ji malamar na cewa, “Ina magana ne a kan mace da bata taɓa sanin namiji ba”,
An kuma ji wata yarinya na cewa ƙawarta, “Banda tsabar sakarci da dolanci, kawai kina zaune sai ya buɗe jaka ya ɗauki breziya?”,
An kuma ji firar wata yarinya da ƙawarta inda suke cewa,
“Ina cikin matsanaciyar damuwa Luba”,
“Cikin dake jikinki wata uku ko?”
“Ya aka yi ki ka sani?”
“Saboda nima na taɓa yi a baya”.
An ji kuma wani aboki yana ce ma abokinsa,
“Na sanka da ‘yanmata had da under age”.
An ga jikar Condom da Cucumber mai
siffar gaban namiji ana nuna su a cikin aji, an ga mata da maza suna raƙashewa
tare a cikin wani shagali da suka shirya, an kuma ga wasu mata suna faɗa har
wata na sunsunar turararen ɗaya, wanda za a iya misalta shi da tarayyar
mace-da-mace amma dai wasu na ganin cewa jarumar cikin Fim ɗin ta sunsuna
turaren abokiyar karawarta ne don ta tantance ƙamshin turaren saurayinta.
Hukumar ta ce fina-finai ta Kano
ta nemi wanda ya shirya Fim ɗin da ma wasu mutane da suka taimaka masa wajen
tsarawa da shirya Fim ɗin, saidai Daraktan ya ce babu wani dalilin da zai sa a
kama shi kuma Fim ɗinsa bai shirya shi don Kanawa ko Hausawa ba, ya shirya shi
ne don ya nusar ya kuma faɗakar da al’ummar Nijeriya, haka kuma ya ce Fim ɗin
ba a Kano ya shiya shi ba, kuma ya yi amfani da harsuna sha bakwai ne wajen
shirya Fim ɗin. Lallai fa an ji ana magana da wasu harsuna a cikin Fim ɗin
kamar Yarabanci da Turanchi kuma an ga wasu fuskoki da ake kyautata zaton ba
Hausawa ba ne, saidai kashi tamanin cikin ɗari na Fim ɗin ya fassara rayuwar
Bahaushe da al’ummar Hausawa ne.
Hukuma tana zarginsa ne da lalata
tarbiya da kuma fitar da Fim ba bisa ƙa’ida ba, wanda ya sa ake nemansa ido
rufe. Shugaban tace fina-finai ta Kano wato Isma’ila Na’abba Afakallah ya ce,
sun aikawa Daraktan domin ya zo ya yi bayanin dalilin da yasa ya fitar da Fim ɗin
ba tare da izininsu ba, amma har zuwa yanzu Daraktan bai je ba.
Daraktan Fim ɗin ya ce fim ɗin ba
yana koyar da ilimin Jima’i ba ne kawai, yana nuna illolin kaciyar mata da kuma
wasu abubuwa da suke faruwa a cikin al’umma. Bidiyon tallar Fim ɗin ‘Makaranta’
ya karaɗe shafukkan shada zumunta ya ja hankali musamman don jin kalmomin da ba
a saba jinsu a cikin fina-finan Hausa ba kamar kalmar Jima’i da bireziya da fant.
0 Comments