8 Janairu, 2022
Daga: Hauwa’u Bello
ABUJA, NIJERIYA –
Rahotanni daga Tillabery da ke yankin Yammacin Ƙasar Nijar ta ce, jami'an tsaro
huɗu sun rasa rayukansu, wasu biyu kuma sun tsira da munanan raunuka a wani
waje inda wata nakiya ta fashe. Ranar juma’a wanda ya yi daidai da 7 ga watan
Janairu shekara ta 2022 ne al’amarin ya faru lokacin da motar sojojin ta taka
wani abu mai fashewa.
Motar ta taka
nakiyar ne tsakanin garuruwan Turundi da Makulandi garuruwan biyu suna cikin
Jihar Tilaberi da ke nesa kaɗan da Birnin Yamai wato babban Birnin ƙasar.
Motar jami'an
tsaron ta taka nakiyar ne a daidai garin Dogon karfe, kuma sakamakon binciken
wucin gadi da jami'an tsaro suka gudanar ya nuna cewa an dasa nakiyar ne.
Wannan sabon
salo na ɗana nakiya da masu tsattsauran ra'ayin kishin Islama ke yi, ya na
haddasa asarar rayuka da dama musamman jami'an tsaro a yankin iyakokin kasashe
uku wato Burkina Faso da Mali da kuma da jamhuriyar ta Nijar.
- An Binne Mutane 143 da Yanbindiga Suka Kashe a Zamfara
- Gobara ta laƙume kasuwar Nguru a Jihar Yobe
- Sheikh Ahmad BUK Ya Rasuwa
Masu tayar da ƙayar
baya dai sun ƙara faɗaɗa hare-harensu inda suke kai wa Jami’an Jamhuriyar Nijar
hari ta hanyar yin kwanton ɓauna ko kuma dasa masu abubuwan fashewa.
0 Comments