Talla

Dattawan Arewa Sun Ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Basu Kunya

Daga: Muhammad Abdallah

KADUNA, NAJERIYA - Ƙungiyar dattawan Arewacin Najeriya wato NEF ta ce, shugaba Muhammadu Buhari ya basu kunya, saboda ya kasa kawo ƙarshen kashe-kashe da ake yi a Arewacin Najeriya.

Mai Magana da yawun ƙungiyar wato Hakeem Baba Ahmed ne ya bayyana haka a taron manema labarai da a kayi a Kaduna ranar Asabar. Hakeem ya ƙara da cewa,

“Shugaba Muhammad Buhari ya yi alƙawarin tabbatar da tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziƙi amma ya kasa yin ko ɗaya”

Ya ƙara da cewa,

 “An gaya wa ’yan Arewa cewa idan Buhari ya zama shugaban ƙasa za a shawo kan matsalolinsu amma komai ya sake taɓarɓarewa a ƙarƙashin mulkinsa, wannan ba farfaganda ba ce; ba almara ba ce, abu ne a zahiri''

Ya ƙara da cewa

“Akwai miliyoyin ƴan gudun hijira a yankin Arewa inda Buhari ya fito sakamakon munanan ayyukan ƴan bindiga, amma gwamnati ta ƙi amincewa da hakan, wannan ba ita ce Najeriyar da muka zaɓa a ƙarƙashin Shugaba Buhari ba?”

Ko baya, bayan nan saida wasu ɓarayi suka kai hari a garuruwan Anka da Shinkafi dake Jihar Zamfara, duk dayake dai Gwamnatin Najeriya tana bakin ƙoƙarinta wajen kawo ƙarshen wannan hare-hare.

A makonnin da suka wuce ne dai, shima Sarki Muhammad Sanusi Lamiɗo ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zaɓi cancanta kar su yi la’akari da jam’iyya ko addini.

Garuruwan Arewacin Najeriya dai kamar su Katsina da Kaduna da Sokoto da Zamfara da Kebbi na ɗaya daga cikin Jihohin da suke fuskantar matsalolin tsaro da ɓarayi masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Wasu Labarai:

  1. Yadda Yan Wasan Najeriya Suka Lallasa Masar da Sudan
  2. Matasa Sune Jigon Siyasa a Kowace Tafiya
  3. Wani Mahaifi Ya yiwa Ƴarsa ƴar Shekara 3 Fyaɗe

Post a Comment

0 Comments