Talla

An Kama Wata Mata Zata Saida Ɗan Kishiyarta

Daga: Muhammad Abdallah

ZAMFARA, NAJERIYA - An kama wata matar da ta yi niyar sayar da ɗan kishiyarta a cikin Jihar Zamfara dake Arewacin Najeriya.

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara ta kama wata mata da take zargi da neman sayar da wani yaro ɗan shekara biyu wanda ake tunanin ɗan kishiyarta ne.

Kwamishinan ƴansanda na jihar wato Ayuba Elkana ya ce, an kama matar ne tun a ranar 8 ga watan Janairu a yankin Tullukawa da ke Gusau inda ake zargin matar da yin aniyar sayar da ɗan kishiyarta.

Matar wadda asalinta mutumiyar ƙauyen Danyade ce da ke Maradi a Jamhuriyyar Nijar, an kama ta ne ɗauke da ɗan kishiyarta wadda ta shaida wa jami'an tsaro cewa ta sato yaron ne daga kishiyarta domin ita ma ta rama sata da sayar da ɗanta da kishiyarta ta yi a can baya.

Amma daga baya ta ƙara shaida wa jami'an tsaro cewa ta yi yunƙurin sayar da yaron ne domin samun kuɗin biyan buƙatunta na yau da kullum.

Rundunar ƴan sandan ta ce za a miƙa wadda ake zargi zuwa ga hukumar kula da shige da fice ta Najeriya domin zurfafa bincike.

Wasu Labarai:

  1. Sojoji Sun Kuɓutar da wasu Matafiya
  2. Wani Bawan allah ya Roƙi QS Yakubu Manni Ya fito Takara
  3. Gwamnati ta Janye Haramcin Amfani da Twitter.

Post a Comment

0 Comments