Talla

Sojojin sun Kashe Alhaji Auta, riƙaƙƙen ɗan fashin dajin Zamfara

Daga: Hauwa'u Bello1 Janairu, 2022

ZAMFARA, NIJERIYA - Dakarun sojin Najeriya sun hallaka wasu riƙaƙƙun ɓarayin daji biyu da suka addabi Jihar Zamfara da Sokoto wato Kachalla Ruga da kuma Alhaji Auta.

An rawaito cewa, ɓarayin biyu sun gamu da ajalinsu ne yayin luguden wutar jiragen sojin saman Najeriya a wasu dazuka da ke ƙauyen Gusami da kuma kauyen Tsamre a karamar hukumar Birnin Magaji.

Kafin mutuwarsu dai suna cikin gawurtattun ƴan fashin dajin da suka addabi Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Wasu majiyoyi sun ce an kuma hallaka yaransu da dama a lokacin hare-haren. 

Ko baya-bayan nan saida wasu mazauna ƙauyukan Zamfara suka yi gudun hijira saboda haraji da ɓarayin ke saka masu. 

Ɓarayin dai sun addabi ƙauyukan da kuma dazukan dake Jihohin Arewa. Watan da ya gabata ne aka ƙone wasu matafiya da suka yi gudun hijira daga garinsu don su gujewa ɓarayin daji. Bayan wannan ne kuma aka samu wata wasiƙa da ake zargin Kachalla ne ya rubuta ta, inda yake neman afuwa ga mutanen Zamfara da Sarkin Musulmi da kuma shugaba Buhari.

Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da harin ɓarayin daji masu sace mutane don karɓar kuɗin fansa. 

A yau dai ne shugaba Buhari ya tabbatarwa da ƴan ƙasa cewa, gwamnati ba za ta saka ido a ci gaba da kashe al'ummar ƙasa ba.

Post a Comment

0 Comments