Talla

Buhari ya tattauna da Ƴan Wasan Super Eagles ta bidiyo

 Daga: Hauwa'u Bello

ABUJA, NAJERIYA - Ƴan wasan na ci gaba sa nuna ƙoƙarinsu wajen cin kofin AFCO. Suna daga cikin ƙungiyoyin kwallon ƙafa na Afrika da suka fi cin kwallaye.

 Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tattaunawa ta bidiyo da ƴan wasan na Super Eagles.

A wani saƙo da Shugaban ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya buƙaci ƴan wasan da su ci gaba da sa ƴan Najeriya farin ciki inda ya ce kada su tsaya a cin wannan wasa na yau kaɗai, su ɗauki kofin baki ɗaya.

Shugaban ya yi magana da kocin Najeriya Augustine Eguavoen da Keftin ɗin ƙungiyar Ahmed Musa da Amaju Pinnick wanda shi ne Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya da jakadan Najeriya a Kamaru Janar Abayomi Olanishakin mai ritaya.

Shugaban ya gode wa kocin Najeriya da sauran muƙarrabansa kan irin jajircewar da suke yi wajen ganin an samu nasara.

Wasu Labarai:

  1. Wani Ɗalibi Ya Kusa Yi Wa Jiniyansa Yankan Rago A Makarantar Kwana Dake Borno
  2. Mayaƙan ISWAP sun sace yara mata da maza 20 a Jihar Borno
  3. Buhari Ya Miƙa Ta'aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa Da Aka Kashe A Kano

Post a Comment

0 Comments