#Arewanews
Daga: Muhammad Abdallah
09 Janairu, 2022
ZAMFARA, NIJERIYA - Shugaban Nijeriya
Muhammadu Buhari ya nemi mutanen Zamfara su ƙara haƙuri, shugaban ya tabbatar
da cewa za su gano waɗanda suke aikata wannan mummunan aiki sannan su ɗaukar
mataki mai tsauri a kansu. Mutanen Zamfara da Sokoto da Kebbi da Katsina da
Kaduna na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin
fansa. Ko satin da ya gabata sai da ɓarayin suka kashe mutane fiye da talatin
da bakwai a ƙauyukan dake cikin Jihar.
A
wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Ƙasar Nijeriya wato Malam Garba
Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya nuna ɓacin ransa matuƙa a kan rahoton da ya
samu kan kisan gillan da aka yi inda ya ce shire-shire ne yasa ɓarayin dajin
suke yin yadda suka so.
Shugaba Buharin ya sake tabbatar
da cewa ɓarayin na gab da zama tarihi a Nijeriya inda ya ce ba za su yi ƙasa a
gwiwa ba a yaƙin da suke yi da waɗannan mutanen da suke kashe mutanen da ba su
ji ba su gani ba.
Wasu
ƙauyuka da ke cikin Jihar Zamfara waɗanda suke Ƙananan Hukumomin Anka da
Bukuyyum da ke Jihar sun binne mutum 143 waɗanda ɓarayin daji suka kashe a
hare-haren da suka kai cikin kwanaki biyu.
Wasu Rahotanni
- Wa Ya Ci Amanar Wani: Gwamna Masari Ko Sanata Babba Kaita?
- Ɓarayi sun sace tsohon jami'in kwastam a Nijeriya
- Fashewar Nakiya Ta Kashe Sojojin Ƙasar Nijar Huɗu
Kodayake,
Gwamnan Jihar wato Gwamna Bello Matawalle ya ce, mutum 36 aka kashe a Ƙaramar
Hukumar Bukkuyum amma zai ziyarci sauran garuruwan don ya tabbatar da cewa ko
iƙirarin da ake yi na kashe sama da mutum 200 gaskiya ne.
0 Comments