Talla

Buhari Ya Miƙa Ta'aziyyarsa Ga Iyayen Hanifa Da Aka Kashe A Kano

 Daga: Muhammad Abdallah

KANO, NAJERIYA - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar yarinyar da Malaminta ya kashe sannan kuma ya jinjina wa 'yansandan Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai shekara biyar. Kisan Hanifa dai wani abun ban tsoro ne, wanda ya tayar da hankullan iyaye tare da ɗalibai waɗanda ke zuwa makarantu don neman ilimi.

Wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawun shugaban ƙasar ya fitar a ranar Juma'a ta ce Buhari ya ce,

 "Hakan zai sa 'yan ƙasa su ƙara amincewa da ayyukan jami'an tsaro".

Shugaba Buhari ya ƙara da cewa, iyaye da kuma 'yan Najeriya da suka dinga bin sawun halin da Hanifa ta shiga sun yi ta fatan za a ceto ta a raye, aikin gano mutanen da jami'an tsaro suka gudanar da ya kai ga gano gawarta abin a yaba ne. ya ƙara da cewa, abu ne da ya kamata ya sa mutane su ƙara yarda da mahukunta.

Shugaban ya ƙara da cewa,

"Duk lokacin da aka samu irin wannan abin alfaharin sai mutane su dinga yabon jami'an tsaro,"

Daga bisani kuma, shugaban ya yi addu’a Allah ya jiƙanta ya kuma ba iyayenta haƙurin rashinta.

A ranar Alhamis ne dai aka gano gawar Hanifa bayan wani malamin makarantarsu ya sace ta a watan Disamba sannan ya kashe tare da binne ta a ɗaya daga cikin gine-ginen makarantar.

Malamin dai ya amsa laifinsa a hannun 'yansanda sannan kuma gwamnatin Jihar Kano da ke Arewacin ƙasar ta rufe makarantar da malamin yake koyarwa.

Kisan Hanifa ya zama wani batun da aka fi tattaunawa a sassa daban-daban na cikin ƙasar, inda iyaye suke alhini tare da jimamin baiwa malamai amanar ya’yansu. Irin wannan salon satar mutanen don karɓar kuɗin fansa bai cika faruwa ba. Haka kuma, malamin ya ɓullo da wani sabon salo ne wanda zai ƙara saka tsoro a zukatan iyayen yara musamman a Arewacin ƙasar inda harkokin tsaro suka taɓarɓare duk da cewa gwamnati da Jami’an tsaro na iya ƙoƙarinsu wajen tabbatar da tsaro.

A shafinsa na fesbuk, ɗansanda mai riƙon gaskiya Haruna Kiyawa ya nuna hoton yadda suka kama Malamin da kuma yadda malamin ya binne gawar Hanifa bayan ya sace ta sai ya kai ta gidansa inda ya ajiye ta tsawon sati biyu, daga nan ne kuma ya bata gubar ɓera tasha ta mutu sannan ya binne ta da taimakonw ani abokinsa a cikin wani kango na makarantar.

An yi ta nuna hotunan Hanifa a kafafen sada zumunta, haka kuma anyi ta yin Allah wadai ga halin rashin tausayi da malamin Hanifa ya nuna.

Wani mai sarhin al’amurran yau da kullum Hamza Adamu Baba Gana da ya fito daga Jihar Gombe ya nuna takaicinsa inda ya yi fata a yanke wa Malamin Hanifa hukuncin ɗaurin rai-da-rai da tare da aiki mai wahala. Ya ce, wannan ne zai ɗanɗana kuɗarsa sosai sannan ya shiga ƙunci da takaici a sauran shekarun rayuwarsa.

Garuruwan Katsina da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da tashe-tashen hankulla, inda ɓarayi ke satar mutane don karɓar kuɗin fansa. Ba a cika samun ɓarayin daji a garin Kano ba, saidai ana yawan samun tsageru masu yin sane da sata da ƙauranci da daba da kwace da satar ɗaiɗaikun mutane don karɓar kuɗin fansa.

Wasu Labarai:

  1. Wata Mata ta Kashe kanta a Kano
  2. An Sace Wani Basarake A Palato
  3. Ɓarayin Daji Sun Kai Sabbin Hare-hare

Post a Comment

0 Comments