Daga: Muhammad Abdallah
4 Janauiru, 2022ZAMFARA, NIJERIYA — Bello Turji shahararren ɓarawo da ya addabi garuruwan
Sokoto da Katsina da Zamfara ya saki wasu mutane da suka daɗe a hannunsa waɗanda
ya sace don karɓar kudin fansa. Ɗan
fashin dajin ya shahara ne sosai a garuruwan dake cikin Jihar Zamfara da Sokoto
wanda ya riƙa sanya haraji a wasu ƙauyuka da ke kusa da dabarsa.
A wani rahoto da aka samu a
Jaridar Dailay Trust, ɓarawon ya sako
mutanen ne ba tare da karɓar ko sisi ba, bisa wani ƙuduri nashi na son kawo
karshen tashe-tashen hankulla da kuma samar da zaman lafiya a garuruwan Zamfara
da Sokoto.
Bello Turji ya sako mutane sannan
ya ajiye su a kusa da ƙauyen Mabera ƙauyen da bai wuce kilomita hudu zuwa
Shinkafi ba, da misalin ƙarfe biyar na marece ne rundunar ‘yansandan dake garin
Shinkafi suka je suka taho da waɗanda aka saki. Daga nan aka wuce da su Gusau. Wasu
daga cikin ‘yanuwan waɗanda aka saki har
sun yi magana da ‘yan’uwansu da aka saka.
Waɗanda aka saki sun tabbatar da
cewa, ba a ba Bello Turji ko sisi ba, ya sako su ne ba tare da ya karɓi kuɗin fansa
ba. Haka kuma, sun tabbatar da cewa ya sako duk waɗanda ya kama don karɓar kuɗin
fansa a ƙoƙarinsa na yin sasanci da hukuma.
A watan da ya gabata ne Bello
Turji ya rubuta wasiƙa zuwa ga Masarautar Shinkafi da Gwamnan Jihar Zamfara da
shugaban Ƙasar Nijeriya bisa ƙudurinsa ne neman afuwa da kuma kawo ƙarshen
sace-sacen da yake yi, kodayake a cikin takardar ya yi iƙirarin cewa shi ne ake
toƙala da faɗa kuma duk a cikin takardar ya buƙaci a sanya shahararren Malamin
nan wato Sheikh Ahmed Gumi wajen yin sasancin, ya ce shi ne ya nemi a saka
malamain domin ya sha zuwa wajensu kuma suna fahimtar koyarwarsa.
Haka kuma, a satin da ya gabata
ne Jaridar PrNigeriya ta ruwaito cewa sojoji sun kashe wasu shahararrun ɓarayin
daji, cikin waɗanda jaridar ta ambata harda sunan Turji, kodayake ba a tabbatar
da cewa an ga gawarsa ba, saidai rahoton ya ce an kashe shi tare da yaransa lokacin
da suka je wata zana’ida ta ɗaya daga cikin giggan ɓarayin.
Jim kaɗan bayan bayyanar rahoton,
sai kuma Jaridar Katsina City News wadda ke yin haɗin guiwa da Jaridar Taskar
Labarai wajen wallafa labarai ta ruwaito cewa, Rugga Kachalla yana nan da
ransa. A cikin ruwayar Jaridar ta ce; Ɗaya
daga cikin ɓarayin da aka ruwaito jirgin sama ya kashe a harin da ya kai a
yankin Zamfara wanda ya yi sanadin kisan Alhaji Auta wato Ruga kacalla, kamar
yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito, Binciken da Jaridun Katsina City News ta
yi a dajin Safana inda Ruga Kacalla ke da ƙarfi ya tabbatar mana Rugga Kacalla
yana nan da ransa. Haka kuma, Alhaji Muhigge wanda shi ne babban yaron Alhaji Ɗan
Auta a yankin Safana shi ma yana nan da ransa.
Garuruwan Katsina da Kaduna da
Zamfara da Sokoto da Kebbi na fama da hare-haren ɓarayin daji masu satar mutane
don karɓar kuɗin fansa.
0 Comments