Labarin Jikokin Sarkin Barayi
Daga:
Littafin Hikimarka Jarinka na Bello Hamisu Ida
An yi wani Sarkin ɓarayi ya
sace ɗiyar wani attajiri, ya tafi da ita wani ƙauye kusa da birnin Katsina, aka
ɗaura masu aure.
Allah ya azurta su da zuriya. Babbar ɗiyarsu Baraka ta yi gadon
sata, ko ɓera albarka. Baraka ta auri wani Mai Kuɗi a birnin Kano, aka kai
amarya ɗakin miji, shekara na zagayowa ta haifi ‘yan-tagwaye aka sanya wa
‘ya’yan Ɗan Hanne da Ɗan Baraka.
Lokacin da suka cika shekara uku, Sarkin Ɓarayi ya zo ya ɗauki Ɗan
Hanne ya tafi da shi ƙauye ya koyi sana’a.
Shi kuwa Ɗan Baraka ya girma wajen mahaifiyarsa, Ɗan Hanne ya tashi
wajen kakansa.
Bayan sheka Goma sha biyar, wata rana talauci ya ishi Sarkin ɓarayi
gashi ƙarfinsa ya ƙare, sai ya ce bari ya jaraba jikansa ko zai iya gadonsa?
Tunda yanzu ya kawo ƙarfi.
Sai ya kira Ɗan Hanne ya aike shi birni ya zambaci wani ɗan birni.
Da Ɗan Hanne ya tashi tafiya sai ya nufi bakin rafi ya samu takardu ya yi masu
linkin kuɗi sannan ya jera su cikin wani ƙaramin akwati ya rufe, ya nufi birni.
Ashe itama Baraka ta aiki Ɗan Baraka ƙauye don ya zambaci wani baƙauye.
Ɗan Baraka kuwa da ya tashi tafiya sai ya samu tsumokarai ya zuba ya ɗaure
cikin wani bargo, ya ɗaure kamar dila, ya ɗauki dila ya nufi ƙauye da nufin ya
yaudari wani ya sayar masa da dilar da kuɗi masu tsoka.
Bisa hanya suka yi kiciɓis da juna! Ɗan Baraka ya yi wa Ɗan Hanne
sallama, ya ce,
“Malam dila ce ta sayarwa in kana bukata.”
‘Banza ta faɗi’ Ɗan Hanne ya ayyana a zuciyarsa, ya ce a bayyane, “Eh,
dama dila za je birni saye.”
“Nawa?” Ya tambaya.
“Fam hamsin da sule
goma.” Ɗan Baraka ya sa suna.
‘In ka sallama fam
talatin sai in ba ka jakar kudina, in ka je gida ka lissafa, ni sauri nake yi”.
Ɗan Hanne ya taya.
Ta faɗi gasassa, ya
yi saurin amincewa, ya karɓi jaka, ya miƙa masa ɗila, cikin sauri kamar mara sa
gaskiya, kowa ya kama hanyar komawa gida murna cike da zuciya.
Ɗan Hanne na isa
gida, ya buɗe dila, sai ya ci karo da tsummokarai yayin da shi kuwa Ɗan Baraka
ya kasa haƙuri, tun a hanya ya buɗe jaka ya ga tulin takardu, cikin fushi ya
ce,
“Ni wannan ɗan ƙauyen zai zambata? Sai na koyar da shi darasi.”
Cikin fushi ya juya ya kama hanya, suka sake haɗuwa, suka ci kwalar
juna, suna cikin faɗa sai ga wasu fatake sun koro raƙuma ɗauke da dukiya, irin
su azurfa, zinare, alkyabba, kwanukan farin ƙarfe da kayan alatu, sun nufi
hanyar shiga birni.
Mazanbatan suka ga faɗa ba nasu ba ne, tunda duk sun fahimci
sana’arsu ɗaya, watau sata, me zai hana su haɗa kai su jaraba sa’a wajen waɗannan
fataken?
Suka amince da wannan shawara su kuwa waɗannan fatake daga Sudan
suke, sun sawo kayan adon Sarakai don su sayar a birni.
Da dare ya tsala ɓarayin
biyu suka yi shigar fataken buzaye suka sauka wajen da fataken Sudan suke, kun san
buzu da shan shayi, buzaye suka aza tukunyar shayi, suka zuba cikin ƙananan
kofuka suka bi fataken suna ba su suna
cewa,
“Yan uwa Musulmi ku sha ku sha shayi, karɓar kyauta tana ƙara imani.”
Su kuwa fatake suka
rinƙa karɓar shayin suna sha, ashe a ɓoye ɓarayin sun sanya banju cikin shayi.
Duk wanda ya sha sai ya ɓingire barci ya ɗebe su.
Da ɗai-ɗaya duk suka yi barci, su kuwa ɓarayi sai suka cire kayan
buzaye suka shiga washe fatake, sai da suka yi masu kaf!
Sannan suka kwashe duk kayan da suka sata suka zuba cikin wata
tsohuwar rijiya dake nesa kaɗan da kasuwa da nufin sai ƙura ta lafa su kwashe
dukiyar.
Gari na wayewa fatake suka tashi suka ga an washe su kaf! suka kai ƙara
wajen sarkin kasuwa, aka baza ‘yan doka suka yi ta bincike har tsawon mako biyu
ba a ji duriyar ɓarayin ba.
Kasuwa ta uku ta zagayo fatake suka
koma inda suka fito. Bayan kasuwa ta huɗu ta ci, da tsakar dare ɓarayi
suka shirya suka tafi bakin tsohuwar rijiyar da suka aje dukiya.
Gardama da kaure tsakanin ɓarayi, wa zai shiga ya ɗebo dukiyar? Kowa
na tsoro kada ɗaya ya ƙulla masa wani tugu in ya shiga cikin rijiya, Saboda kowa
neman sa’ar ɗaya yake ya kai shi ƙiyama don ya gaje dukiyar shi kaɗai.
Daga ƙarshe aka sa wa ɓarawon ƙauye igiya ya shiga cikin tsohuwar rijiya, shi kuwa ɓarawon birni ya zura babban masaki, ɓarawon ƙauye ya rinƙa zuba dukiya cikin masakin shi kuwa ɓarawon birni yana jawowa yana fiddo ta waje.
Wasu Labarai
Ɓarawon ƙauye ya ce, “Ta kusa ƙarewa.” Saboda yana sane da tugunsa,
da ya tabbata dukiyar ta ƙare sai ya ce, “Wacce zan ɗauro ita ce ta ƙarshe,
tana da nauyi, sai ka yi a hankali.”
Cikin farin ciki ya ce, “Yi maza ka ɗauro ta duka, zan iya jawo ta.”
Yana zura masaki sai ɓarawon ƙauye ya samu wani bargo ya lulluɓe duk
jikinsa ya shige cikin masaki. Ɓarawon birni ya jawo masaki ya kai ma’ajiya ya
aje duk da masaki, ya dawo bakin rijiyar ya mirgina wani murgujejen dutsi cikin
rijiya, ya tabbatar da ya mutu, sai ya yi hamdala dukiya ta zama tasa shi kaɗai.
Shi kuwa ɓarawon ƙauye ko da aka ajiye shi, sai ya fito ya jiɗe duk
akwatunan, ya kamo wasu jakuna da suke kiwo, ya ɗora masu akwatuna ya kora suka
shige daji.
Ɓarawon birni na zuwa cikin kango sai ya ga wayam! Ya tabbata ɓarawon
ƙauye ne amma duk inda ɗan ƙauye yake ba ka raba shi da jaki wajen ɗaukar kaya,
cikin sauri sai ya shiga daji yana kukan jaki,
“Um! Umm! Ummm!.”
Shi kuwa ɓarawon ƙauye da ma bai yi nisa ba, da ya ji kukan jaki sai
ya ce, “yauwa! Ga wani jaki can ya gudo bari in tara ko na ƙara samun mataimaki.”
A tara! a tara! Sai suka haɗe kowa ya yi cirko-cirko, suka yi wa
juna zuru! Ɓarawon birni ya ci kwalar ɓarawon ƙauye ya ce, “Baƙauyen banza, ni za
ka zamba ta?”
Ɓarawon ƙauye bai yi wata-wata ba ya yayibi kafafuwan ɓarawon birni
ya yi sama da su ya wurgar! Ji kake ricaa! Nan kokowa ta kaure suka shiga
jibgar juna.
Gab da Asubahi, yan-doka sun fito, suka yi ram! Da ɓarayin biyu. Da
bincike ya tsananta aka gane ashe ma Ɗan Hanne da Ɗan Baraka ne ɓarayin, kayan
da suka sata kuwa na fatake ne, aka nemo su har garuruwansu aka damƙa masu
dukiyarsu. Ɓarayin kuwa aka kai su gidan yari.
0 Comments