Daga: Muhammad Abdallah
ABUJA, NAJERIYA - Wasu ɓarayin daji sun kai wasu sabbin hare-hare a wasu yankunan Jihar Nija. Harin ya zo ne jim kaɗan bayan shugaban ƙasa ya ƙaddanar da rundunar fatattakar ɓarayin daji.
Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da kaiharin amma ba ta kai ga ba da adadin waɗanda harin ya rutsa da su ba. Tuni dai gwamnatin Najeriya ta ayyana ɓarayin dajin a matsayin ƴan ta'adda, duk da haka ɓarayin dajin na ƙara faɗaɗa hare-harensu a garuruwan Nija.
Wani mutum mai suna Malam Abdulkadir Muhamad Beri, mazaunin jihar ya ce, ko a ranar Lahadin nan da ta gabata sai da suka fafata da waɗannan ‘yan fashin daji.
Musa Bawa kuma, shi ne kwamandan ‘yan sa kai a yankin na Beri ya tabbatar da cewa ɓarayin na ta ƙara kai sabbin hare-hare tun bayan ayyana su a matsayin ƴan ta'adda.
Ko a yankin ƙaramar Hukumar Shiroro an tabbatar da cewa ɓarayin sun kai sabbin hare-hare, inda a wajen hare-haren da suka kai an yi asarar rayuka da kuma dukiyoyi.
Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da kai sabbin harin, amma sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ya ce, yawan mutanen da aka ba da labarin an kashe bai kai haka ba.
Masu sharhi a kan sha'anin tsaro suna ci gaba da bayyana buƙatar ƙara matsa ƙaimi domin kakkaɓe waɗannan ‘yan ta’adda.
Garuruwan Katsina da Kaduna Zamfara da Sokoto da Kebbi da Niger na daga cikin garuruwan dake fama da tashe-tashwn hankulla da ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa.
Wasu Labarai:
0 Comments