8 Janairu, 2022
Daga: Hauwa’u Bello
ABUJA, NIJERIYA
- Wasu mutane da ake zargin ɓarayin daj ne masu satar mutane don karɓar kuɗin
fansa sun sace wasu mutume biyar a hare-hare daban-daban da suka kai a ƙananan
hukumomi biyu na Jihar Kwara.
A
cikin rahoton da aka samu a Channels TƁ ya ce, harin na farko ya faru ne a
Egbejila da ke kan hanyar ƙauyen Obate a Ƙaramar Hukumar Asa. A wajen harin an
sace wani tsohon mataimakin kwanturola na kwastam mai suna Mohammed Zarma, an ɗauke
tsohon kwasam ɗin ne a gonarsa inda yake kiwon kifin zamani. Wasu rahotanni sun
ƙara da cewa, ɓarayin sun shiga gonar ne da bindigogi ƙirar AK-47 inda suka tafi
dashi cikin daji.
Wasu Rahotanni
- Fashewar Nakiya Ta Kashe Sojojin Ƙasar Nijar Huɗu
- An Binne Mutane 143 da Yanbindiga Suka Kashe a Zamfara
- Gobara ta laƙume kasuwar Nguru a Jihar Yobe
Wani
hari makamancin wannan ya faru ne a kan hanyar Obo Aiyegunle zuwa Osi da ke
Jihar Ekiti inda ɓarayi suka sace wani bakanike da matarsa mai ciki da kuma
wasu mutum biyu da ke koyon sana'ar kanikanci.
0 Comments