Daga: Muhammad Abdallah
ABUJA, NAJERIYA - 'Yan bindiga sun sace wani Basarake mai suna Gyang Balak a jihar Filato. Sarki Da. Gyang Balak Gut yakasance mai faɗa aji a gundumar Gwom Rwei Vwang da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
A sace Basaraken ne a daidai makarantar National Institute for Policy and Strategic Study (NIPSS) kuru inda ɓarayin suka yi shinge, bayan sun sacw shi sun nemi basu kuɗi miliyan goma a matsayin kuɗin fansa.
Wani Ɗan Majalisar ne dake wakiltar ƙaramar hukumar a majalisar dokokin jihar ya bayyana yadda aka sace shi.
Jaridar Punch ta ruwaito ɗan majalisar inda yake cewa,
An sace basaraken ne a ranar Lahadin data wuce da misalin karfe 8 na dare.
Rahotanni sun ce an sace shi ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida a kan titin dake yankin Kuru.
Ba wannan lokacin bane aka fara sace sarakuna, ko a watan da ya gabata, wasu 'yan bindigar sun sace wani basarake a karamar hukumar Mangu wanda daga bisani suka sake shi bayan biyan kuɗin fansa.
Garuruwan Katsina da Zamfara da Kaduna da Sokoto da Kebbi da Neja na daga cikin garuruwan da sula fi samun matsalar ɓarayin daji masu satar mutane don karɓar kuɗi fansa.
Shugaban ƙasa ya ƙaddamar da rundunar fatattakar daji wadda ya ba umurni su kakkaɓe barayin dajin dake Neja. Hukumomi suna yi bakin ƙoƙarinsu wajen kawo ƙarshen kashe-kashe da ake yi a Arewacin Najeriya.
Wasu Labarai:
0 Comments