KATSINA, NAJERIYA - An roƙi Q'S Mannir Yakubu da ya yi ma Allah Ya yi ma Annabi da ya taimaki jihar Katsina ya tsaya takarar Gwamna a shekarar 2023.
Al'ummar Jihar Katsina suna buƙatar Dattijo Jajirtacce mai Ilimin boko da Addini, Mai kishin Al'umma ba mai Kishin Aljihunsa shida Iyalansa ba, Ya zo Ya gaji Maigirma Gwamna Aminu BELLO MASARI daga Inda Ya tsaya na Bunƙasa ƙasa da inganta rayuwar Al'ummar Jihar Katsina.
Alhaji QS MANNIR YAKUBU FNIQS Al'ummar Jihar Katsina sun shedeka da irin Hakurinka da dattakunka wajen kowane Al'amari na rayuwar duniya.
Kaine Mataimakin Gwamnan na farko mai Hakuri da biyayya ga megidansa batareda masayar miyon baki koda da second 1.
Kaine Mataimakin Gwamnan na farko Mai Aqida irinta siyasa da iya salon Jagorantar Al'umma kuma asamu nasara cikin Yardar Allah (SWT).
Kaine Mataimakin Gwamnan na farko da Allah Ya kafaka acikin Jam'iyyar da baka Taba yin wata Jam'iyya ba face Wannan Jam'iyyar Bisa Gaskiya da rikon Amana.
Al'ummar Jihar Katsina Suna Yabawa da Baiwar Ilimin Boko dana Addini da Allah (SWT) Yabaka kuma kake tafiya dasu wajen gudanar da Al'amuran Jagorancinka.
Al'ummar Jihar Katsina Sun Shedeka Cewa Maigirma Gwamna RT HON AMINU BELLO MASARI baitaba Saka ka cikin wani Al'amarin aiki na Cigaba a Jihar nan, batared ansamu abunda akesoba cikin Yardar Allah (SWT).
Al'ummar Jihar Katsina sun Shedeka akan Jajircewa Wajen aiki babu fafa lolo, babu Jinkiri, Babu kwange badan komaiba saidan sanin Mahimmacin aiki da riko da gaskiya akan Aikinka.
Dukda Lokaci Bazai bari Mufadi Tarin Dinbin Alkairan da Allah (SWT) Ya horeka dasu badan kafi kowa iyawa ba, Saidan Yardarsa. Dahak muke Maka Fatan Alkairi Dan Allah (SWT) Kataimaka Ka Amsa Kiran Al'ummar Jihar Katsina mai Albarka.
Muna rokon AlLah (SWT) Yabamu Zaman Lafiya da Kwanciyar Hankali a Fadin Jihar Katsina da Nigeria .
Allah (SWT) Yayi mana Maganin duk wata masifa ka kawo mana karshen ta Saboda kima da Mutuncin Annabi Muhamad (SAW)
Wasu Labarai:
0 Comments